Kasuwanci
Gwamnati Ta Sa Wutar Lantarki Ta Amfani Da Hasken Rana A Kasuwar Dutsen Jigawa
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa.
Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta gudanar, ya hada shaguna 300 da wutar lantarki daga na’urorin hasken rana da aka sanya a cikin kasuwar, inda kowane shago kuma an saka masa fanka amfani da hasken rana kyauta.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da kasuwar a hukumance, Malam Umar Namadi ya ce shirin zai saukaka harkokin kasuwanci, da rage kashe kudi, da kuma bunkasa ribar ‘yan kasuwa.
Ya kuma yi alkawarin kafa fitilun masu amfani da hasken rana a kasuwar domin inganta tsaro, sannan ya bayyana wasu matakai na tallafa wa ‘yan kasuwa a jihar Jigawa, wadanda suka hada da samar da reshen bankin masana’antu (BOI) a jihar da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da bankin, inda gwamnatin jihar ta zuba naira biliyan 4 domin tallafa wa masu kananan sana’o’i.
Namadi ya kuma bukaci ’yan kasuwa a jihar da su yi amfani da wannan wurin su samu kudaden da kungiyar ta BOI ke da su don fadada kasuwancinsu.
A nasa jawabin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar Jigawa Alhaji Yahaya Ibrahim ya yabawa gwamnan bisa samar wa kasuwar wutar lantarki da hasken rana da kuma shirye-shiryen karfafawa ‘yan kasuwa daban-daban.
Ya kara da cewa aikin samar da wutar lantarkin kasuwar ya kasance farkon shirin Gwamna Namadi ga ‘yan kasuwa a jihar.
Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wani bangare na aikin, na sanya na’urar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya kaddamar da shi a shekarar da ta gabata yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar, kuma a lokacin gwamnatin jihar ta yi alkawarin sa wutar a rumfuna kowa da kowa.
USMAN MZ
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
