Labarai
Gwamnan Zamfara Na Karbar Bakuncin Gwamnonin PDP
Gwamna Dauda Lawal na karbar bakuncin gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP don wani muhimmin taro a jihar Zamfara.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta nuna cewa a yau Juma’a ne ake sa ran gwamnonin za su isa Gusau gabanin taron da aka shirya yi a ranar Asabar.
A cewar sanarwar, kungiyar gwamnonin PDP za ta yi amfani da taron ne domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi siyasa, karfafa hadin kan jam’iyya, da kuma lalubo hanyoyin samar da ci gaba na hadin gwiwa a jihohinsu.
Gwamna Dauda Lawal ne zai shirya wa gwamnonin da suka ziyarce liyafar cin abincin dare, yayin da za a yi zaman sirri a gobe.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, gwamnonin za su kuma magance muhimman batutuwan da suka shafi shirye-shiryen taron jam’iyyar na kasa da aka shirya gudanarwa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.
REL/AMINU DALHATU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
