Connect with us

Labarai

Gidauniyar Matasa Ta Maigatari Za Ta Shuka Tsirai 1,600 A Kokarinta Na Kare Muhalli

Published

on

Gidauniyar Matasa ta Maigatari a Jihar Jigawa ta ce za ta shuka tsirrai 1,600 a daminar bana a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinta na kare muhalli.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan wani taron da suka gudanar, shugaban ƙungiyar, Muktari Muhammad Maigatari, ya bayyana cewa Gidauniyar Masarautar Gumel ce ta bayar da tsirran kyauta.

A cewarsa, nau’ukan tsirran sun haɗa da Dalbejiya, Bishiyar Zogale,  Dorawa da sauransu.

Muktari Maigatari ya ce, domin tabbatar da nasarar shirin a yankin, an kafa kwamitoci biyu — ɗaya na rabawa da zaɓen wuraren shuka, ɗayan kuma na bibiyar ci gaban tsirran da sauran ayyuka.

Ya ce gidauniyar ta samo tsirran ’ya’yan itatuwa da suka haɗa da gwaiba, lemu, da gwanda domin shukawa.

Ya bayyana godiya ga iyalan Kanal Sani Bello mai ritaya bisa bayar da gudummawar naira dubu ɗari biyar (₦500,000) domin sayen kwanduna na musamman don kare tsirran.

Mukhtar Maigatari ya kuma gode wa masu ruwa da tsaki, jagororin gidauniyar, da al’ummar Maigatari bisa goyon bayan da suka bayar wajen tabbatar da nasarar shirin.

 

Usman Mohammed Zaria

 

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara