Labarai
Gwamnonin Najeriya Sun Bayyana Alhininsu Bisa Rasuwar ‘Yan Wasan Kano
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana alhininta bisa rasuwar wasu ‘yan wasa daga jihar Kano a wani hadarin mota.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya fitar, ya ce hadarin ya faru ne yayin da tawagar jihar ke dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala a jihar Ogun.
Kungiyar ta NGF ta mika ta’aziyyar ta ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar Kano,da ma kasa baki daya.
Kungiyar ta roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ji kan ‘yan wasan, Ya kuma ba iyalansu hakurin jure wannan babban rashi.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
