Labarai
Gwamna Umar Namadi Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Sallah Karama
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar.

Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan na Ramadan.

Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa shugabanni jagorancin don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma.

Namadi ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Radiyon Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamnan ya kuma karɓi manyan baki da suka kai masa gaisuwar Sallah a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
