Fasaha
NAFDAC Ta Kaddamar Da Sabbin Shirye-Shiryen Yaki Da Jaribun Magunguna
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta sake jaddada aniyar ta na dakile yaduwar magungunan jabun a fadin kasar nan.
Darakta Janar na Hukumar Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye ta bayyana hakan a yayin bikin bude taron wayar da kan jama’a na kwanaki biyu da aka gudanar a Kano.
Farfesa Mojisola Christianah wacce Darakta Pharmacist, Pharmacist Bitrus Fraden ta wakilta ta ce NAFDAC ta bullo da wasu sabbin tsare-tsare guda uku da nufin inganta hanyoyin magance yaduwar magungunan jabu a kasar.
Babban Daraktan ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su tallafa wa wadannan tsare-tsare, da nufin tabbatar da samar da ingantattun kayayyakin kiwon lafiya, masu inganci ga ‘yan Nijeriya.
Ta ce Najeriya ita ce kasa ta farko a Afirka da ta fara amfani da wannan fasahar, wanda ke baiwa masu ruwa da tsaki damar ganowa da kuma watsi da kayayyakin da basu da inganci.
“Dokar hukumar kula da lafiyar yara ta NAFDAC mai lamba 2024 wata ka’ida ce ta musamman da ke magance bukatu na musamman na yara. Wannan ka’ida ta ginu ne a kan tsarin rijistar da ake da shi, yana ba da karin kariya don tabbatar da tsaro da ingancin kayayyakin kiwon lafiya ga yara.”
A nata bangaren wata mataimakiyar darakta Regina Garba ta ce makasudin taron shi ne wayar da kan masu ruwa da tsaki kan hadin gwiwa ta wannan fanni.
Ko’odinetan NAFDAC na shiyyar Arewa maso Yamma Mista Fadi Nantim Mullah ya ce makasudin gudanar da taron bitar a shiyyar ya kasance ne saboda yawaitar masu sana’ar magunguna musamman a Kano.
Abdullahi Jalaluddeen Kano
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
