Ilimi
An Yabawa Darikar Tijjaniyya akan Samar da Hadin kai a Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba da irin gudunmawar da darikar Tijjaniyya ke bayarwa wajen samar da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmin kasar nan.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron Mauludin bana 2025 na marigayi Sheikh Ibrahim Nyass, jagoran darikar Tijjaniyya a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.
Mataimakin wanda ya samu wakilcin Alhaji Babagana Fannami, Ya yabawa kungiyar musulmi bisa tsayin daka a tsawon karnukan da suka gabata akan koyarwar addinin musulunci na gaskiya.
Shettima wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya yaba da tsarin jagoranci na darikar ‘Sufi’ ga bil’adama.
Babban bako na musamman ya jaddada irin tsayin dakan da darikar Tijjaniyya ke da shi wajen koyi da darussan rayuwan Annabi Muhammad ba tare da tauye lamuran fikihu na Musulunci ba.
Don haka ya tunatar da musulmi da su yi koyi da koyarwa ta gaskiya ta Musulunci, su guje wa tsatsauran ra’ayi.
Hakazalika babban mai masaukin baki Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba da kokarin Darikar Tijjaniyya wajen wanzar da zaman lafiya da zumunci da sauran kungiyoyin a Najeriya.
“A matsayina na mai masaukin baki, dole ne mu yaba muku da kuka zo Kano daga nesa da kusa domin halartar mauludin bana na Sheik Ibrahim Nyass.”
Mai Martaba Sarkin Kano na 16 Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, ya yi addu’ar samun hadin kan musulmin duniya baki daya da kuma hakuri da sauran mabiya addinai.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai2 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai4 hours agoAKCILS Ta Karrama Jami’in Tsaro Bayan Shekaru 22
-
Labarai2 days ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
