Connect with us

Labarai

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gano Wani Shirin Tayar Da Tarzoma A Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’an tsaro a jihar Kano  sun gano wani rahoton sirri da ke nuna cewa wasu bata gari na shirin kaddamar da tarzoma a  muhimman wurare da suka hada da  majalisar dokokin jihar  da wasu gine-ginen gwamnati.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammad Usaini Gumel ne ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar ‘yan sandan Kano.

Ya ce jami’an tsaro na hadin gwiwa za su rika gudanar da bincike gida-gida domin bankado duk wanda ke tunanin ya fi karfin hukuma.

CP Mohammed Usaini Gumel ya ce hukumomin tsaro za su tsaya tsayin daka wajen bin doka, kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bin umarnin kotu.

Ya kuma baiwa jama’a tabbacin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma baki daya.

CP Mohammed Usaini Gumel ya bukaci jama’a da su yi kokarin bayar da hadin kai da nufin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa an yi zanga-zanga a Kano, inda ya ce ba gaskiya ba ne, kuma jita-jita ce ta wasu bata gari da ke da mugun nufi ga ci gaban jihar.

 

Abdullahi Jalaluddeen

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara