Connect with us

Labarai

Tangardar Da Jingin Singapore Ya Samu A Sama Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutum Daya, Yayin Da 30 Su Sami Rauni

Published

on

Fasinja daya ya mutu wasu sama da 30 sun ji rauni a cikin wani jirgin sama na ƙasar Singapore da zai koma ƙasar daga London, bayan da ya gamu da mummunar gargada a sama.

Sakamakon lamarin an karkatar da jirgin ƙirar Boeing 777-300ER zuwa Bangkok, inda ya sauka a can.

Jirgin mai lamba SQ 321 yana ɗauke da fasinja 211 da ma’aikatansa 18 kamar yadda wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar ta bayyana.

Ana can ana ci gaba da kula da wadanda suka ji raunin da taimakon hukumomin Thailand, inda aka tashi wata tawaga ta musamman ta ma’aikatan lafiya daga Singapore din domin ba su kulawa.

Zuwa yanzu ba a san takamaimai abin da ya faru a cikin jirgin ba bayan da ya gamu da gargadar a sama.

Abu ne da aka saba jirgi ya gamu da gargada a sama, to amma irin wannan mai tsanani ba kasafai ake haduwa da ita ba.

Wani lokaci akan iya hasashen gargadar – kuma matuka jirgin sama su kan aika da sako ga takwarorinsu da ke hanya domin gargaɗinsu, to amma kuma matsalar kan faru kwatsam – kuma za ta iya faruwa a ko’ina kuma a kodayaushe.

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara