Connect with us

Kasuwanci

Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe – KANUPDA

Published

on

 

Manajan Daraktan Hukumar Tsare-tsare da Ci gaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Architect Ibrahim Yakub Adamu ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu ya saba wa sashe na 11,12 da 13 na dokar KNUPDA za a gurfanar da shi a gaban kuliya.

 

 

A cewarsa, gargadin ya zama wajibi ganin yadda ake samun karuwar gine-gine ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba.

 

 

Manajan daraktan ya bukaci jama’a da su samu takardar izinin gini daga KNUPDA kafin su fara kowane irin gini.

 

 

Architect Ibrahim ya yi nuni da cewa gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta saukaka hanyoyin samun takardar izinin gini a jihar.

 

 

“Kwanan nan an samarda wata na’ura da za ta gaggauta ba jama’a takardar izinin gini ba kamar da a da sai an dauki watanni kafin a kammala aikin.”

 

 

Sai dai ya jaddada cewa masu neman izinin gini su kuma gabatar da zane kafin zuwa neman iznin don kwaucewa rugujewar gini a nan gaba.

 

Manajan daraktan ya lissafo jerin matakan da KNUPDA ta dauka don tabbatar da cikakken bin al’umma.

 

 

Ya bayyana abin takaicin da ya faru a baya-bayan nan a matsayin sakaci domin tun da farko KNUPDA ta ba su takardar su dakatar da aikin ta daya da ta biyu kafin ginin ya ruguje.

 

 

 

Architect Yakubu Adamu ya kuma bayyana cewa an gudanar da tarurruka tare da hadin gwiwar jami’an tsaro domin gano wanda ya gina shi tare da gurfanar da shi.

 

 

Architet Ibrahim ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rigamu gidan gaskiya tare da addu’ar Allah ya wadanda suka sami rauni lafiya.

 

 

KHADIJAH ALIYU/Wababe

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara