Connect with us

Labarai

Gwamnatin Katsina Ta Dakatar Da Sarkin Daura Tare Da Kafa Kwamitin Bincike

Published

on

Daga Isma’il Adamu 

Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar,  daga gudanar da dukkan harkokin aikinsa da kuma tafiye-tafiye sakamakon zargin cin zarafi da wata ‘yar  yawon buɗe ido ta yi a kansa.

Gwamnatin ta kuma kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan zargin da aka bayyana a wani saƙo da aka wallafa a kafafen sada zumunta tare da wani bidiyo.

A  wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Bala Zango, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta ce Gwamna Dikko Umar Radda ne ya bayar da umarnin kafa kwamitin domin binciken lamarin da kuma ba gwamnati shawarwarin da suka dace.

Sanarwar ta bayyana cewa za a ci gaba da dakatar da harkokin Sarkin  da tafiye-tafiyensa har zuwa lokacin da kwamitin zai kammala bincikensa.

Gwamnatin ta tabbatar wa al’umma cewa za a tabbatar da adalci, sannan za ta aiwatar da sakamakon binciken kwamitin da shawarwarin da zai bayar.

Ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda, tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana sunayen mambobin kwamitin ba, ko lokacin da ake sa ran za su gabatar da rahoton bincikensu ba.

Fassara: Safiyah Abdulkadir 

Labarai

Labarai21 minutes ago

Gwamnatin Katsina Ta Dakatar Da Sarkin Daura Tare Da Kafa Kwamitin Bincike

Daga Isma’il Adamu  Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar,  daga gudanar da dukkan harkokin...

Labarai1 hour ago

Gwamna Namadi Ya Bukaci Al’ummar Jihar Jigawa Su Cigaba Da Mara Masa Baya

Daga Usman MZ  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da amincewa da...

Labarai4 days ago

INEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna

Daga Abdullahi Shettima Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen jihar Kaduna, ta kaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwar...

Labarai4 days ago

An Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki

An bukaci masu aikin kula da lafiyar al’umma da su kasance masu bin ka’idojin sana’arsu tare da kiyaye martabar aikin,...

Labarai5 days ago

NIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo

Daga Usman Muhammad Zaria  Cibiyar Nazarin Kimiyyar Dabbobi ta Ƙasa (NIAS) ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da...

Labarai6 days ago

Gobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara

Daga Ali Muhammad Rabi’u  Wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta ƙona shaguna takwas da shagunan kwantena guda...

Labarai6 days ago

Shugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo

Daga Khadijah Aliyu Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya ƙaddamar da sabon ofishin ’yan sanda na shiyya...

Labarai1 week ago

Jigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a

Daga Usman Muhammad Zaria  Mukaddashin Babban Alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Jigawa, Umar Nasir Ahmad, ya fara...

Labarai1 week ago

Za a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna

Hukumar Zaɓe ta Jihar Kaduna (KADSIECOM) ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar a...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu

Daga Sani Dutsinma  Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin halartar gangamin yaƙin...

Mafi Shahara