Labarai
Gwamna Namadi Ya Bukaci Al’ummar Jihar Jigawa Su Cigaba Da Mara Masa Baya
Daga Usman MZ
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da amincewa da gwamnatinsa gabanin babban zaben shekarar 2027, yana mai tabbatar musu cewa za a saka musu da kyakkyawan shugabanci bisa goyon bayan da suke bayarwa.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a yayin wani gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a karamar hukumar Gwiwa, inda ya nuna godiyarsa bisa dimbin jama’ar da suka halarta.
Ya ce karuwar goyon bayan da jam’iyyar ke samu a yayin gangamin da take gudanarwa a matakin kasa ya nuna irin amincewar da al’umma suke da ita ga APC, yana mai alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin tabbatar da wannan amana.
Da yake kwatanta tarbar da aka yi masa a Gwiwa da wadda aka yi masa a karamar hukumar Roni a ranar Lahadi, Gwamna Namadi ya ce yawan jama’ar da suka halarta ya ba shi mamaki matuka.
Ya tabbatar wa al’ummar cewa gwamnatinsa ba za ta ba su kunya ba, yana mai kira gare su da su ci gaba da kasancewa tare da jam’iyyar.
Gwamnan ya kuma karbi sama da mambobi 850 daga jam’iyyun ADC da PDP, wadanda suka sauya sheka zuwa APC daga dukkanin mazabu 11 na karamar hukumar Gwiwa.
Da yake tarbar wadanda suka sauya shekar, Namadi ya tabbatar musu da cewa za a ba su dama da kulawa yadda yakamata, ba tare da la’akari da lokacin da suka shiga ba.
Ya kuma bukace su da su yi amfani da kwarewarsu ta siyasa da alakar da suke da ita da al’umma wajen jawo karin mambobin jam’iyyun adawa zuwa APC.
Da yake magana a madadin wadanda suka sauya shekar, Malam Tijjani, tsohon mamban PDP, ya ce sun yanke shawarar shiga APC ne sakamakon kyakkyawan shugabancin da suka ce Gwamna Namadi yake yi.
Ya kuma tabbatar wa gwamnan da shugabannin APC cewa za su himmatu wajen wayar da kan jama’a da neman goyon baya ga jam’iyyar domin samun nasara a babban zaben 2027.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa gwamnan ya kuma kaddamar da fara aikin gina wata hanya da karamar hukumar Gwiwa ta bayar da kwangilarta.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai5 days agoNIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo
-
Labarai6 days agoGobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara
-
Labarai6 days agoShugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo
-
Labarai4 days agoINEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna
-
Labarai4 days agoAn Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki
-
Labarai21 minutes agoGwamnatin Katsina Ta Dakatar Da Sarkin Daura Tare Da Kafa Kwamitin Bincike
