Labarai
Gwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu
Daga Sani Dutsinma
Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Yakubu Ahmed BK ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
Ya ce shugabancin APC, jami’an gwamnati da ƙungiyoyin goyon bayan jam’iyyar na ci gaba da aiki kafa da kafa da masu ruwa da tsaki a faɗin jihar domin tabbatar da nasarar gangamin.
Ahmed BK ya bayyana cewa APC ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris na da cikakken kwarin gwiwa kan goyon bayan da take samu daga al’umma da kuma kyakkyawar alaƙarta da su.
Ya tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa zai ziyarci jihar da gwamnatinta da al’ummarta ke yabawa da jagorancinsa, tare da nuna goyon baya ga nasarar ajandar Renewed Hope.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga mambobin APC, magoya bayanta, masu ruwa da tsaki da sauran mazauna Jihar Kebbi da su fito cikin lumana domin tarbar Shugaban Ƙasa yadda ya kamata.
Ya buƙace su da su nuna haɗin kai, karamci da kuma jajircewa wajen ci gaban jam’iyyar da ƙasa baki ɗaya.
Ahmed BK ya ƙara da cewa gwamnatin APC ta ci gaba da ƙarfafa tsarin jam’iyyar a ƙananan hukumomi 21 na jihar ta hanyar haɗin kai, shawarwari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Ya ce gangamin shugaban ƙasar da ke tafe zai ba jam’iyyar wata dama ta ƙara ƙarfafa matsayinta da kuma kyautata alaƙarta da al’umma.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai5 days agoJigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a
-
Labarai3 days agoNIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo
-
Labarai4 days agoGobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara
-
Labarai4 days agoShugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo
-
Labarai1 day agoINEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna
-
Labarai5 days agoZa a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna
-
Labarai2 days agoAn Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki
