Labarai
Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
Daga Khadijah Aliyu
Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka lalace, waɗanda Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayen Kaya ta Jihar Kano (KCPC) ta ƙwace saboda barazanar da suke yi ga lafiyar jama’a.
Umarnin kotun ya biyo bayan shigar da ƙara da hukumar ta yi, bayan gano garin alkamar da ya lalace, wanda ake zargin an tanade shi ne domin sayar wa jama’a.
Hukumar ta ce ta ƙwace buhunan ne bayan samun bayanan sirri kan adana wasu buhuna masu yawa na fulawa da suka lalace, waɗanda aka shirya rabawa da sayarwa ga masu saye.
Da yake magana kan lamarin, Shugaban hukumar, Dakta Ibrahim Garba Muhammad, ya jaddada aniyar hukumar na tabbatar da bin dokokin kare haƙƙin masu sayen kaya da kuma tilasta wa ‘yan kasuwa bin ƙa’idojin kasuwanci.
Ya bayyana cewa gurfanar da ‘yan kasuwar da suka karya dokokin kare masu saye yana da muhimmanci wajen kare al’ummar jihar daga amfani da kayayyakin da ba su da aminci ga lafiya da sauran harkokin kasuwanci marasa adalci.
Dakta Garba ya buƙaci ‘yan kasuwa da su ba hukumar haɗin kai, yana mai cewa babban aikin hukumar shi ne tabbatar da bin doka da kare masu saye daga cutarwa.
Ya kuma yaba wa al’umma bisa ƙara wayewa kan ayyukan hukumar, tare da ƙarfafa musu gwiwar duba ingancin kaya, ranar ƙarewar amfaninsu da bayanan da ke jikin marufinsu kafin saye.
Shugaban Hukumar ya kuma gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ci gaba da tallafa wa hukumar, yana mai bayyana cewa haɗin kan gwamnatin jihar na taimakawa wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Ana sa ran umarnin kotun zai hana sake shigar da fulawar cikin kasuwa, tare da kare masu saye daga haɗarin matsalolin lafiya.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai2 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai1 day agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
-
Labarai1 day agoArewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari
