Kasuwanci
Nijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa
Daga Shindong Bala, Kaduna
Nijeriya za ta fara kera makamai da sauran kayayyakin tsaro , domin amfanin ƙasar da kuma fitar da su zuwa ƙasashen waje, musamman sauran ƙasashen Afirka.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ne ya bayyana hakan a wajen buɗe bikin baje kolin kayayyakin tsaro na farko a Afirka, wanda aka gudanar a Legas.
Wata sanarwa da Babbar Jami’ar Yaɗa Labarai ta Ma’aikatar Tsaro, Queenet Iheoma-Hart, ta sanya wa hannu, ta ce ministan ya yi kira ga masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje da su yi amfani da damar bikin wajen zuba jari a masana’antar tsaro ta Najeriya.
Janar Christopher Musa ya jaddada cewa kera kayayyakin tsaro a cikin gida zai ƙarfafa ƙarfin tsaron ƙasar, tare da samar da damarmaki don bunƙasa tattalin arziki da ci gaba.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya a shirye take ta kulla haɗin gwiwa a fannin tsaro, bisa amincewa da juna da kuma mutunta juna.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa barazanar tsaro na ƙara rincabewa, lamarin da ke buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka da ƙwararrun masu ƙirƙirar fasahohi a duniya.
Ya yi kira ga abokan hulɗa a fannin tsaro da masu ƙirƙirar basirar AI da sauran sabbin fasahohi da su haɗa kai da Najeriya wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin nahiyar Afirka.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya buƙaci mahalarta taron da su yi amfani da bikin wajen musayar ilimi, gudanar da tattaunawar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe biyu, sanya hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna da kuma bincika damarmakin zuba jari a Najeriya.
Darakta-Janar na Kamfanin Masana’antar Tsaro ta Najeriya, Manjo Janar B. I. Alaya, ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa ci gaba da goyon bayan da yake bai wa kamfanin, tare da alƙawarin ƙara ƙarfin samar da kayayyakin tsaro.
Bayan kammala bikin buɗe taron, ministan tsaron ya zagaya rumfunan baje kolin kayayyaki, inda aka nuna kayayyakin tsaro daga ƙasashe daban-daban. Haka kuma, ya gudanar da wani babban taron tattaunawa da Kwamandan Rundunar Sojin Amurka mai kula da Afirka (United States Africa Command).
Baje kolin, wanda ya haɗa masu ruwa da tsaki a fannin tsaro daga Najeriya da sauran ƙasashe, na da nufin inganta haɗin gwiwa, ƙirƙira da bunƙasa fasahohi, da kuma jawo zuba jari a fannin tsaro.
Taron ya samu halartar Babban Hafsan Tsaron Najeriya, hafsoshin rundunonin soji masu kan aiki da waɗanda suka yi ritaya, shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, da kuma wakilai daga ƙasashen Afirka sama da 20.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoRundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar da Rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka
-
Labarai3 days agoSu Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma
-
Labarai3 days agoBa Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba — Ministan Yada Labarai
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Nadin Kwamishinoni Shida
-
Kasuwanci3 days agoTsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa
-
Labarai2 days agoMutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya
-
Labarai2 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jiha
-
Labarai2 days agoKatsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya
