Labarai
Kachalla Ɗan Ƙarami Ya Kashe Abokin Gabarsa A Zamfara

Kasurgumin dan ta’addar da ya addabi yankin Batsari a Jihar Katsina da wani yanki na Jihar Zamfara ya gamu da ajalinsa a hannun Kachalla Dan Karami.
Wata majiya mai tushe daga Batsari a Jihar Katsina ta tabbatar mana da cewa Kachalla Dan Karami ya fille kan Dangote ne a wani mummunan faɗa da aka gwabza a Dunmurun da ke Karamar Hukumar Zurmi a Zamfara.
Kachalla Dankarami ya yi sanadiyar kashe Dangote ne tare da wasu kannensa guda biyu da ke addabar Jihar Katsina da wani yanki na Jihar Zamfara a safiyar ranar Lahadi da ta gabata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Dan Karami da tawagarsa sun yi wa Dangote da yaransa kwanton ɓauna ne a daren Asabar, inda suka fara gwabzawa har safiyar ranar Lahadin da ta gabata.
Wata majiya daga jami’an tsaro ta bayyana mana cewa tun da farko dai yaran Dangote ne suka kashe yaron Kachalla Dan Karami sakamakon sace musu tumaki da aka yi.
“Abin da ya faru shi ne, ɗaya daga cikin yaran Dan Karami ya saci garken tumakin ɗaya daga cikin ’yan uwan Dangote, Sale Lamo, sai yaran Dangote suka bi sawun tumakin suka karɓo su, sannan suka kashe yaron.”
“A lokacin da abin ya faru Dan Karami yana wani gari da ake kira Rukudawa, sai aka ba shi labarin abin da ya faru, kuma ya yi azama ya taho domin ɗaukar fansa.
“Da ya isa Dumburum, sai ya ji an ce Dangote ya yi shiri zai zo ya yaƙe shi, daga nan ne ya yanke shawara, ya yi musu kwanton ɓauna, ya samu sa’ar kashe Dangote da yaransa Lamo na Balewa da Usman Yalo.”
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
