Connect with us

Labarai

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Published

on

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna

Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a cikin shirye-shiryen tallafa wa ci gaban yankin, tana mai cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne ginshiƙan samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa mai ma’ana.

Babban Daraktan Gudanarwa na hukumar, Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyin jama’a kai tsaye ta wayar tarho a cikin shirin Sashen Hausa Radio Nijeriya Kaduna Hannu Da Yawa na tsawon sa’o’i biyu.

Farfesa Ma’aji ya ce shirye-shiryen tallafa wa ci gaban yankin na hukumar za su shafi muhimman fannoni da suka haɗa da ilimi da kiwon lafiya da noma da kare muhalli da samar da ayyukan yi, da kuma ƙarfafa gwiwar matasa da mata.

Ya bayyana cewa rashin tsaro na haifar da mummunan tasiri ga ci gaba ta fannoni daban-daban, musamman ta hanyar hana manoma zuwa gonakinsu da kawo cikas ga harkokin kasuwanci da shafar halartar ɗalibai a makarantu, da kuma takaita damar zuba jari.

Ya ce: “Taimakawa wajen dawo da tsaro a yankin Arewa Maso Yamma shi ne babban fifikonmu a cikin shirye-shiryen tallafa wa ci gaba. Ba za mu iya samun ci gaba a fannin ilimi da noma ko masana’antu ba, matuƙar al’ummarmu ba za su iya zuwa gonakinsu ko su kwanta barci cikin kwanciyar hankali ba.”

Dangane da fannin ilimi, shugaban hukumar NWDC ya sanar da cewa za a gudanar da gagarumin aikin inganta gine-ginen makarantu a faɗin jihohi bakwai na yankin, ciki har da gyaran gine-ginen makarantu da suka lalace da samar da kayan koyarwa na zamani.

Ya ce: “’Ya’yanmu na karatu a ƙarƙashin bishiyoyi da kuma gine-ginen da suka lalace. Hukumar za ta gyara makarantu tare da samar da kayan koyarwa na zamani, domin bai wa yaranmu ingantaccen ilimin da ya dace da su.”

A wani mataki na bunƙasa harkokin tattalin arziki da samar da ayyukan yi, Farfesa Ma’aji ya bayyana shirin kafa banki a matsayin wani aikin hukumar, tare da ƙoƙarin farfaɗo da masana’antun da suka daina aiki a faɗin yankin.

Ya ce: “Muna shirin kafa wani banki da hukumar za ta mallaka a matsayin wani reshe nata. Haka kuma, za mu farfaɗo da sauran kamfanonin da suka daina aiki a yankin. Wannan zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin yankin tare da samar da dubban ayyukan yi ga ɗimbin matasanmu.”

Ya ƙara da cewa hukumar na tattaunawa da masu zuba jari daga cikin Najeriya da wajen ƙasar, domin bunƙasa damar noma da Kuma dinbin al’ummar da ake dasu don samar kuɗi da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

Ya ce: “Muna gayyatar masu zuba jari daga cikin ƙasa da wajen ƙasa. Yankin Arewa Maso Yamma yana da albarkar filayen noma masu faɗi da kuma ƙwararrun ma’aikata. Muna son mayar da wannan dama zuwa arziki.”

Babban jami’in hukumar ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin hukumar da gwamnatocin jihohi da sarakunan gargajiya da shugabannin ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, domin cimma manufofin ci gaban hukumar.

Ya ce: “Muna buƙatar goyon bayan gwamnoninmu da sarakunanmu na gargajiya da kuma dukkan attajirai maza da mata ‘yan asalin Arewa Maso Yamma.

Sarakunan gargajiya da attajirai da masu ilimi suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tabbatar da nasarar wannan hukuma.”

Farfesa Ma’aji ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa kafa hukumar, yana mai bayyana hakan a matsayin wani mataki da ya zo a kan lokaci domin magance matsalolin ci gaban da suka daɗe suna addabar yankin.

Ya ƙara da cewa: “Dole ne mu yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesansa na kafa wannan hukuma. Yanzu muna buƙatar addu’o’in kowa da kowa domin tabbatar da nasararmu.”

Masu kiran waya da suka bada tasu gudummuwa a shirin sun buƙaci shugabannin hukumar da su sauke nauyin da ke kansu cikin gaskiya da riƙon amana da tsoron Allah.

Haka kuma, sun yi kira da a ci gaba da mai da hankali kan matsalar rashin tsaro da ƙalubalen da ake fuskanta a fannonin kiwon lafiya da ilimi, da kuma rashin aikin yi da ke addabar al’ummomi a faɗin yankin Arewa Maso Yamma.

Mohammed Aminu Abdullahi (Gombi) da Umar S. Fada ne suka jagoranci shirin.

 

Bayan kammala shirin, Mukaddashin Daraktan Shiyya ya zagaya da Farfesa Ma’aji a harabar gidan rediyon Najeriya Kaduna, inda suka duba wasu wurare da aka gano suna buƙatar ɗaukar matakan gaggawa na gyara. Daga nan ne suka wuce zuwa wani taron sirri.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Labarai7 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai9 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara