Connect with us

Labarai

Zafin Rana Na Addabar Al’ummar Kano

Published

on

Mazauna Kano na ci gaba da fama da matsanancin zafi da ya mamaye birnin tare da jefa lafiyar jama’a cikin haɗari. Yanayin zafin da ake fuskanta ya sa rayuwa ta yi matuƙar wahala ga mutane da dama a cikin birnin da kewaye.

Rahotanni sun nuna cewa zafin rana a Kano na kaiwa kusan digiri 45 na Celsius da rana, yayin da dare ma ba ya sauka sosai saboda yanayin zafi da ke ci gaba har zuwa wayewar gari. Hakan ya sa mutane da yawa ke fama da rashin samun isasshen barci.

Kasuwanni da makarantu da ofisoshi da hanyoyi sun cika da jama’a masu zufa yayin da suke ƙoƙarin gudanar da harkokinsu cikin yanayi mai tsanani. Sai dai kaɗan daga cikin mutane ne ke samun sauƙi a wuraren da ake amfani da na’urorin sanyaya iska.

Mafi yawan al’umma kuwa na komawa gidajensu da fatan samun sauƙi amma rashin wutar lantarki da ƙarancin iska a gidaje da cunkoso na ƙara tsananta matsalar. Mata da yara na daga cikin waɗanda zafin ya fi shafa musamman a unguwannin da ba su da ingantattun hanyoyin sanyaya muhalli.

Wani mazaunin Kano, Abubakar Salihu, ya bayyana cewa mutane kaɗan ne kawai ke iya amfani da na’urar sanyaya iska a duk dare, yayin da wasu ke kwana a saman rufi ko a waje domin neman iska. Ya ce iyalai da dama na kwana cikin rashin barci har zuwa asuba.

Ita ma Grace Tanko ta ce tsananin zafin ya sauya tsarin barcinta tare da janyo mata gajiya da ciwon jiki saboda rashin samun hutun da ya dace da dare.

Masu sana’ar sufuri ma sun bayyana cewa zafin rana ya fara shafar lafiyarsu. Wani direban adaidaita sahu, Umar Muhammad, ya ce tsawon lokacin da suke yi a rana mai zafi tare da rashin barci da dare na janyo musu matsalolin lafiya.

A ƙauyukan Kano kuwa, matsalar tsaro ta hana mutane kwana a waje kamar yadda aka saba a baya saboda tsoron hare-haren ‘yan bindiga. Wasu mazauna sun ce yanzu sun fi son jimre wa zafi a cikin gida fiye da fuskantar haɗarin tsaro a waje.

Masana lafiya sun gargadi jama’a cewa tsananin zafi na iya haddasa matsaloli kamar bugun zafi da ciwon kai da jiri da zazzaɓi. Likita a Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano, Dakta Uba Sani, ya shawarci jama’a su riƙa yawaita shan ruwa da kauce wa yawan fita rana tare da neman kulawar likita idan matsalar ta tsananta.

Khadijah Aliyu/Kano

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara