Kasuwanci
Kyari Ya Yi Alkawarin Ci Gaba
Dan takarar kujerar wakilan tarayya mai neman wakiltar ƙananan hukumomin Mobbar da Abadam da Guzamala da Kukawa a Jihar Borno, Mohammed Abba Kyari, ya yi alkawarin samar da ingantacciyar wakilci idan aka zaɓe shi.
Ya bayyana hakan ne bayan karɓar fom dinsa a hedikwatar jam’iyyar ADC da ke Abuja, inda ya nuna kwarin gwiwar samun nasara.
Mohammed Abba Kyari ya ce ya shiga takarar ne domin kawo ci gaba da shugabanci nagari tare da magance matsalolin tsaro da ilimi da lafiya da tallafa wa matasa da bunƙasa ababen more rayuwa.
Ya kuma yi alƙawarin yin aiki tare da masu ruwa da tsaki da mata da matasa domin tabbatar da an wakilci muradun al’umma yadda ya kamata a majalisar wakilai.
Bashir Mayere/Abuja
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
