Ilimi
Gwamna AbdulRaza ya jajanta wa Oke Ode, da sauran al’ummomi kan hare-haren masu garkuwa da mutane
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan.
A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.
Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, sannan kuma ya baiwa al’umma tabbacin dawo da zaman lafiya cikin kankanin lokaci.
Sanarwar ta kuma aike da sakon ta’aziyya da jaje ga daukacin al’ummomin da aka samu cikin wannan rikici — daga Ifelodun zuwa Irepodun, Isin, Ekiti, Edu, da Patigi.
A cewarsa ana tanadin komai don rage illar hare-haren da kuma tabbatar da kawo karshen irin wadannan abubuwan.
A yayin ziyarar Gwamnan yana karbar bayanai daga jami’an tsaro da wasu masu ruwa da tsaki daga Oke Ode da Igbaja makwabciyarta, ciki har da shugaban kungiyar ci gaban Oke Ode na kasa, Alhaji Abdulganiyu Ajala; Dattijo Oyin Zubair, da shugaban matasa.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
