Ilimi
An Hori Musulmai Su Nuna Halin Dattako Da Tawali’u
An shawarci Musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye na tawali’u kamar yadda Annabi Muhammadu ya yi misali da su don yin rayuwa mai inganci.
Babban Limamin Masallacin Darul Khair Imam Abdulmumini Abdulrafiu-Onilaru ya bada nasihar ne a cikin hudubar Juma’a da ya gabatar a garin Ilorin na jihar Kwara.
Ya ce yin rayuwar da za ta yi tasiri kai tsaye ga wasu za ta jawo lada mai kyau daga Allah.
A cewarsa ana sa ran musulmi za su gudanar da rayuwarsu daidai da koyarwar Alkur’ani da Hadisin Annabi Muhammad.
Imam Abdulrafiu-Onilaru ya bukaci al’ummar musulmi da su kasance masu kula da ‘yan uwansu da kuma taimaka wa mabukata.
Ya kuma yi kira gare su da su mutunta ji da ra’ayin jama’a domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a cikin al’umma
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
