Connect with us

Labarai

Majalisar Jigawa Ta Yi Karatu Na Biyu Kan Dokar Fansho Ga Tsofaffin Shugabanni

Published

on

Kudirin gyaran dokar  fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa.

Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari.

Alhaji Hamza Adamu Ibrahim ya yi bayanin cewar, daga cikin shugabanin da suka rike mukaman siyasa da ya kamata su amfana da irin wannan fansho sun hada da Gwamna da Mataimakan Gwamna da Shugaban Majalisar Dokoki da Kuma alfarmar da ya kamata su ci gaba da samu bayan sun bar mulki.

Bayan Akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar, ya gudanar da karatu na 2 akan kudurin sai Shugaban Majalisar Dokokin jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya kafa Kwamati na musamman mai Wakilai 7 da za su zagaya wasu daga cikin jihohin kasar nan domin gano yadda dokar ta ke aiki a wadancan jihohi.

Shugaban Masu Rinjaye na majalisar Kuma wakilin mazabar Roni, Alhaji Lawan Muhammad Dansure shi ne shugaban Kwamatin, yayin da wakilin mazabar Malam Madori Alhaji Hamza Adamu Ibrahim da na mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari da mazabar Fagam Alhaji Yahaya Zakari Kwarko da na mazabar Taura, Alhaji Dayyabu Shehu da na mazabar Kaugama Alhaji Sani Sale Zaburan da na mazabar Bulangu Alhaji Yusuf Ahmad Soja su ka kasance wakilan kwamatin.

An bai wa Kwamatin mako 4 domin ya gudanar da wannan aiki sannan ya mika rahoton sa ga zauren majalisar dokokin jihar jigawan.

 

Usman Mohammed Zaria

Labarai

Labarai8 hours ago

Gwamnatin Katsina Ta Dakatar Da Sarkin Daura Tare Da Kafa Kwamitin Bincike

Daga Isma’il Adamu  Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar,  daga gudanar da dukkan harkokin...

Labarai9 hours ago

Gwamna Namadi Ya Bukaci Al’ummar Jihar Jigawa Su Cigaba Da Mara Masa Baya

Daga Usman MZ  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da amincewa da...

Labarai4 days ago

INEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna

Daga Abdullahi Shettima Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen jihar Kaduna, ta kaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwar...

Labarai5 days ago

An Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki

An bukaci masu aikin kula da lafiyar al’umma da su kasance masu bin ka’idojin sana’arsu tare da kiyaye martabar aikin,...

Labarai5 days ago

NIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo

Daga Usman Muhammad Zaria  Cibiyar Nazarin Kimiyyar Dabbobi ta Ƙasa (NIAS) ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da...

Labarai7 days ago

Gobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara

Daga Ali Muhammad Rabi’u  Wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta ƙona shaguna takwas da shagunan kwantena guda...

Labarai7 days ago

Shugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo

Daga Khadijah Aliyu Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya ƙaddamar da sabon ofishin ’yan sanda na shiyya...

Labarai1 week ago

Jigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a

Daga Usman Muhammad Zaria  Mukaddashin Babban Alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Jigawa, Umar Nasir Ahmad, ya fara...

Labarai1 week ago

Za a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna

Hukumar Zaɓe ta Jihar Kaduna (KADSIECOM) ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar a...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu

Daga Sani Dutsinma  Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin halartar gangamin yaƙin...

Mafi Shahara