Connect with us

Kasuwanci

Neja Za Ta Kaddamar da Ayyukan Jiragen Sama Daga Filin Jirgin Sama na Bola Ahmed Tinubu.

Published

on

Gwamnatin jihar Neja za ta fara gudanar da zirga-zirgar jiragen sama daga sabon filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu da aka kaddamar a Minna, tare da kamfanin Overland Airways Limited.

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in kula da zirga-zirgar jiragen sama na Overland, Captain Edward Boyo ya raba wa manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.

 

Ya bayyana cewa an shirya fara jigilar jiragen a ranar 23 ga Afrilu, 2025, wanda zai hada Minna zuwa Abuja da Legas, manyan biranen siyasa da kasuwanci na Najeriya.

 

Kyaftin Boyo ya bayyana cewa, haɗin gwiwa da kamfanin na Overland Airways—kamfanin jiragen sama masu zaman kansu mafi dadewa a Najeriya—yana wakiltar wani muhimmin ci gaba na aiwatar da tsarin raya ababen more rayuwa na Gwamna Bago da kuma sanya jihar Neja a matsayin cibiyar sa hannun jari, kasuwanci, da yawon buɗe ido.

 

“Mun yi farin cikin zabar mu a matsayin kamfanin da zai kaddamar da wannan aiki mai dimbin tarihi, “Wannan hidimar tana kara jaddada kudurinmu na fadada hanyoyin sadarwa a fadin Najeriya da kuma hada hannu da gwamnatoci masu hangen nesa kamar jihar Neja domin kawo ci gaba kusa da jama’a, saboda haka muna jinjina wa Gwamna Bago da tawagar NNA kan wannan jajircewa da kawo sauyi.” Ya bayyana.

 

Tun da farko, babban jami’in gudanarwa na hukumar ta NNA, Alhaji Liman Katamba Kutigi ya ce, “Wannan shirin ya wuce hanyar jirgin sama— gada ce ta samun dama. Ta hanyar hada kai da kamfanin jiragen sama na Overland, muna kafa wani sabon tsari na hada-hadar zirga-zirgar jiragen sama na yankin, tare da aminci da tasirin tattalin arziki.

 

A cewarsa, wannan shi ne mafarin babban ajandar mayar da jihar Neja a matsayin wata babbar mai taka rawa a harkokin sufurin jiragen sama da na Najeriya.”

 

A cewar tsare-tsare Tsarin Jirgin kamar haka; Minna – Lagos – Minna: Litinin, Laraba, Juma’a, yayin da ita

Tashi daga Legas zuwa Minna: 8:00 na safe

Tashi daga Minna zuwa Legas: 3:00 na yamma

Minna – Abuja – Minna: Litinin, Laraba, Juma’a da kuma tashi daga Minna zuwa Abuja: 9:30 na safe haka kuma ya tashi daga Abuja zuwa Minna: 2:00 na rana.

 

Saboda haka, Overland Airways an san shi da kyakkyawan yanayin tafiye-tafiye na yanki, zai yi amfani da waɗannan jiragen ta hanyar amfani da sabon jirginsa na Embraer E-175, kuma kamfanin jirgin ya kiyaye IATA Operational Safety Audit (IOSA) rajista tun 2015 kuma yana aiki da rundunar jiragen ruwa da suka haɗa da Embraer jets, ATR-42s, ATR-42s, ATR-72s da kuma ATR-70D.

 

PR ALIYU LAWAL.

Labarai

Labarai1 day ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai2 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai2 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai2 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai3 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara