Ilimi
Gwamnatin Kano Ta Bullo Da Sabbin Hanyoyin Kare Makarantunta Daga Kalubalen Tsaro
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta dauki wani muhimmin mataki na tabbatar da tsaron makarantunta, inda za a hada hannu da masu ruwa da tsaki don kara karfafa tsaro a yankunan da makarantu suke.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin bude taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a jihar da kuma horas da jami’an tsaron makarantu, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan wanda kwamishinan Ilimi Alhaji Ali Haruna Makoda ya wakilta, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki kudirin gwamnatinsa na bunkasa fannin ilimi a jihar.
Ya ce yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar kalubale wajen tabbatar da tsaro a makarantu, wannan shirin wani muhimmin mataki ne na karfafa tsaro da inganta yanayin koyo.
A jawabinsa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abayomi Shogunle, ya jaddada muhimmancin tsaro a makarantun, inda ya bayyana cewa abu ne da gwamnati mai ci ta ba da fifikoa kai.
Ya yi nuni da cewa, Sifeto janarna ‘yan sanda ne ya kaddamar da rundunar tsaro ta makarantu da nufin magance matsalolin tsaro a makarantun firamare da sakandare da manyan makarantu.
Shi ma a nasa jawabin mataimakin shugaban jami’ar Aliko Dangote, Farfesa Musa Tukur Yakasai, ya yabawa horon kan inganta tsaro a cibiyoyin ilimi.
Tun da farko Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun, wanda mataimakin sufeto janar shiyya ta daya AIG Ahmad Ammani ya wakilta, ya jaddada muhimmancin hada hannu tsakanin jama’a da jami’an tsaro domin magance matsalar rashin tsaro a makarantu da cibiyoyi.
Taron mai taken “Karfafa Tsaro da Hadin Kan Al’umma wajen Kare Ilimi,” ya hada wakilai daga ‘Yan sandan Najeriya, da rundunar Soji, da cibiyoyin ilimi da dai sauransu.
Taron ya samu halartar shugabannin hukumomin tsaro na Kano da sauran masu ruwa da tsaki.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
