Labarai
Manyan Attajiran Duniya Sun Halarci Bikin Auren Dan Wani Attajiri A Indiya
Wasu daga cikin manyan masu fada a ji a duniya sun isa jihar Gujarat ta kasar Indiya domin halartar bikin auren mutum mafi dukiya a nahiyar Asiya.
Daga cikin bakin akwai shugaban facebook Mark Zuckerberg da shahararriyar mawakiya Rihanna da tsohon wanda ya fi kowa arziki a duniya Bill Gates.
Dukkanin su sun halarci walimar da Mukesh Ambani, shugaban rukunin kamfanonin Reliance Industries, kuma attajiri mafi dukiya a nahiyar Asiya ya shirya domin murnan bikin auren dan shi.
Matashi Anant Ambani, mai shekara 28 a duniya zai auri masoyiyarsa Radhika Merchant a cikin watan Yuli.
Shahararrun ‘yan wasan fina finan Indiya, Shah Rukh Khan da Amitabh Bachchan na daga cikin wadanda suka halarci walimar ta kwana uku wadda ta gudana a birnin Jamnagar.
Yanzu haka Mukesh Ambani, mai shekara 66 a duniya shi ne mutum na 10 a jerin mutane mafiya kudi a duniya, inda dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 115, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.
Mahaifin Mukeh Ambani ne ya kafa rukunin kamfanin Reliance Industries a shekarar 1966, wanda katafaren rukunin kamfanoni ne da ya kunshi hadawa da sayar da kaya daban-daban sai kuma harkar hada-hadar kudi da na sadarwa.
Anant Ambani shi ne dan’auta a cikin ‘yayan mahaifin nasa uku, wadanda dukkanin su suke cikin manyan shugabannin rukunin kamfanonin na Reliance Industries.
Matashin na aiki a bangaren kasuwancin makamashi na rukunin kamfanonin kuma yana cikin shugabannin da ke tafiyar da lamurran gidauniyar rukunin kamfanonin.
Wannan kasaitacciyar walimar aure ta ji da gani daya ce daga cikin irin su da iyalan na Ambani suka yi kaurin suna wajen shiryawa.
A shekarar 2018, shahararriyar mawakiyar Amurka, Beyonce na daga cikin wadanda suka cashe a walimar daurin auren ‘yar Mista Ambani, Isha Ambani, wanda aka yi a birnin Udaipur. Tsofaffin sakatarorin harkokin waje na Amurka Hillary Clinton da John Kerry na daga cikin wadanda suka halarci walimar ta wancan lokaci.
Wani rahoto na kafar yada labaru ta Bloomberg a wancan lokaci ya kiyasta cewa an kashe kudi dalar Amurka miliyan 100 a lokacin bikin – sai dai wani ‘na kusa da iyalin Ambani’ ya musanta batun, inda ya ce kudin da aka kashe bai wuce dala miliyan 15 ba.
Walimar ta wannan karo ta fara ne daga farkon wannan mako, inda iyalin na Ambani suka raba abinci ga al’ummar garin Jamnagar.
Sauran bakin da aka gani wurin taron sun hada da maidakin tsohon shugaban Amurka, Ivanka Trump, da tsoffin firaministocin Canada da Autralia, wato Stephen Harper da Kevin Rudd.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
