Labarai
Jagororin Cibiyar NIPR Sun Kai Ziyarar Ta’aziya Ga Gwamna Namadi Na Jigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya tarɓi jagorancin Cibiyar Masu Harka da Yan Jaridu ta kasa (NIPR) a Gidan Gwamnati dake Dutse.
Ayarin, wanda Shugaban Cibiyar na ƙasa kuma shugaban majalisar ke jagoranta, ya kai ziyarar ce domin mika ta’aziyya bayan rasuwar mahaifiyar gwamnan, Hajiya Maryam Namadi, da ɗansa, Abdulwahab Umar Namadi.
Dr. Ike Neliaku ya isar da sakon jinjina daga Cibiyar NIPR da mambobinta na ƙasa, yana mai bayyana babban rashin da gwamna da iyalinsa suka fuskanta.
Ya jaddada goyon bayan su da haɗin kai a wannan lokacin na alhini, tare da yi wa waɗanda suka rasu addu’a.
A nasa tsokacin, Gwamna Umar Namadi ya yi godiya matuka ga Dr. Neliaku da jagorancin Cibiyar NIPR sakamakon nuna damuwa da haɗin kai.
Ya bayyana cewa zai kasance mai rikewa tare da dabbaka dankon zumunci a tsakanin jagororin Cibiyar.
Radio Najeriya ya ruwaito cewa an yi wa jagorancin Cibiyar ta NIPR gaisuwa tarba da abinci a dakin taro na gidan gwamnati.
Jagororin Cibiyar NIPR sun isa Dutse a shirye-shiryensu na karrama gwamna Namadi a matsayinsa na mai gudanar da harkokin cibiyar.
COV/USMAN MZ
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
