Connect with us

Labarai

NIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Cibiyar Nazarin Kimiyyar Dabbobi ta Ƙasa (NIAS) ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da lambar yabo ta girmamawa ta musamman, bisa ƙoƙarin gwamnatinsa na bunƙasa harkar kiwo.

An miƙa masa lambar yabon ne yayin ziyarar ban girma da tawagar cibiyar, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Farfesa Suleiman Elias Bogoro, ta kai masa a gidan gwamnati da ke Dutse.

A cewar wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, Farfesa Bogoro ya bayyana Jigawa a matsayin jiha abin koyi a ƙasar nan wajen bunƙasa harkar kiwo, bisa manufofi da zuba jari da gwamnatin ke yi.

Ya bayyana wasu daga cikin nasarorin gwamnatin, da suka haɗa da kafa ma’aikatar kula da harkokin kiwo, buɗe sashen nazarin kimiyyar dabbobi a Jami’ar Sule Lamido da kuma ɗaukar nauyin jami’an fasaha 16 zuwa ƙasar Indiya domin samun ƙarin horo na musamman.

Sauran ayyukan sun haɗa da yarjejeniyar zuba jarin dala miliyan 10 da kamfanin Srinivasa Farms domin bunƙasa kiwon kaji, tallafa wa zawarawa 2,350 ta hanyar shirin kiwon awaki da kuma aikin bunƙasa gonar ciyawar kiwo mai faɗin hekta dubu 100.

Farfesa Bogoro ya ce cibiyar NIAS a shirye take ta tallafa wa jihar a fannonin inganta abincin dabbobi, tantance ƙwararru, daidaita ma’auni da horas da ma’aikatan harkar kiwo.

A nasa jawabin, Gwamna Namadi ya gode wa cibiyar bisa karramawar, inda ya bayyana ta a matsayin ƙarfafa gwiwa wajen ci gaba da bunƙasa harkar kiwo. Ya ce shirin gwamnatin na da manufar inganta samar da abinci, samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnan ya tabbatar wa cibiyar cewa gwamnatinsa za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da ita, tare da alƙawarin samar da fili domin gina ofishin NIAS a jihar. Ya kuma ce kasafin kuɗin shekarar 2027 zai tanadi makudan kuɗaɗe domin bunƙasa harkar kiwo.

Fassara: Safiyah Abdulkadir 

Labarai

Labarai1 day ago

INEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna

Daga Abdullahi Shettima Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen jihar Kaduna, ta kaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwar...

Labarai2 days ago

An Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki

An bukaci masu aikin kula da lafiyar al’umma da su kasance masu bin ka’idojin sana’arsu tare da kiyaye martabar aikin,...

Labarai3 days ago

NIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo

Daga Usman Muhammad Zaria  Cibiyar Nazarin Kimiyyar Dabbobi ta Ƙasa (NIAS) ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da...

Labarai4 days ago

Gobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara

Daga Ali Muhammad Rabi’u  Wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta ƙona shaguna takwas da shagunan kwantena guda...

Labarai4 days ago

Shugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo

Daga Khadijah Aliyu Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya ƙaddamar da sabon ofishin ’yan sanda na shiyya...

Labarai5 days ago

Jigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a

Daga Usman Muhammad Zaria  Mukaddashin Babban Alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Jigawa, Umar Nasir Ahmad, ya fara...

Labarai5 days ago

Za a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna

Hukumar Zaɓe ta Jihar Kaduna (KADSIECOM) ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar a...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu

Daga Sani Dutsinma  Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin halartar gangamin yaƙin...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Don Bunƙasa Kiwo Da Sana’o’i

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.124 domin ginawa da gyara cibiyoyin kiwo...

Labarai1 week ago

Tinubu Ya Gargadi ’Yan Siyasa Kan Tashin Hankali Gabanin Zaɓen 2027

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan guje wa tashin hankali,...

Mafi Shahara