Labarai
Jigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a
Daga Usman Muhammad Zaria
Mukaddashin Babban Alƙalin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Jigawa, Umar Nasir Ahmad, ya fara ziyarar aiki a kotunan Shari’a da ke faɗin jihar, domin sanin halin da kotunan ke ciki da kuma ƙarfafa gwiwar ma’aikata wajen inganta ayyukansu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Abbas Rufa’i Wangara ya bai wa gidan Rediyon Najeriya a Dutse, ya bayyana cewa zuwa yanzu, ziyarar ta kai shi kotunan Shari’a da ke Kado-Wawa, Bulangu, Kafin-Hausa, Auyo da Hadejia.
A yayin ziyarar, Umar Nasir Ahmad ya jaddada aniyar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a, ta kula da walwala da bunƙasa ƙwarewar ma’aikatan kotuna.
Ya bayyana cewa ƙarfafa gwiwar ma’aikata na da muhimmanci wajen tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da shari’a.
Mukaddashin Babban Alƙalin ya buƙaci ma’aikatan da su kasance masu jajircewa, ladabi da riƙon amana w
ajen gudanar da ayyukansu, yana mai tunatar da su cewa bai kamata su ci amanar amincewar da al’umma ta yi musu ba.
Yayin ziyarar tasa ya samu rakiyar Magatakardar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a, Barrister Kabiru Abubakar Gumel; Babban Jami’in d je Kula da Kotunan Shari’a, Barrister Isma’il Sani; da mataimakinsa na Shiyyar Hadejia, Barrister Isyak Mohd, da sauran manyan jami’an kotun.
Abbas Rufa’i Wangara ya ce ana sa ran za a ci gaba da ziyarar zuwa sauran kotunan Shari’a da ke faɗin jihar, inda Mukaddashin Babban Alƙalin ya tabbatar da cewa bayanan da za a tattara yayin ziyarar za su taimaka wajen jagorantar sauye-sauyen da ake gudanarwa domin ƙarfafa tsarin shari’a a Jihar Jigawa.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai3 days agoNIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu
-
Labarai4 days agoGobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara
-
Labarai4 days agoShugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo
-
Labarai1 day agoINEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna
-
Labarai5 days agoZa a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna
-
Labarai2 days agoAn Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki
