Nishadi
Katu tace a duba lafiyar Kwakwalwar Murja Kunya

Wata kotu da ke zaman ta a birnin Kano ta bayar da umarnin tura ƴar tiktok Murja Ibrahim Kunya zuwa asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta.
Mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Babajibo Ibrahim ne ya tabbatar wa BBC hakan bayan zaman kotun da aka yi a yau Talata.
Babjibo ya ce “yanayin da take ciki da kamannunta da kuma maganganun da take faɗa sun nuna cewa ba ta cikin hali na cikakken hankali.”
Ya ƙara da cewa “wannan ne dalilin da ya sa alƙalin ya buƙaci a tura wadda ake zargin zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa har zuwa ranar 20 ga watan biyar, 2024.”
Hukumar Hizba ta jihar Kano ce ta kama Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami’an tsaro bisa zargin ta da laifukan da suka shafi baɗala a shafukan sada zumunta.
Kwamandan hukumar ta Hizba a jihar, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al’umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al’umma, kawo ɓata-gari cikin unguwa da kuma iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.
Batun kamawa da tura fitacciyar ƴar tiktok ɗin zuwa gidan yari ya ja hankalin al’ummar a jihar ta Kano.
Haka nan labarin fitar da ita daga inda kotu ta tura ta, wato gidan gyaran hali shi ma ya janyo muhawara mai zafi a jihar.
A ranar Litinin gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba ta da hannu a sakin ƴar tiktok ɗin daga gidan yari bayan umarnin da kotu ta bayar na tsare ta.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York