Labarai
Shugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo
Daga Khadijah Aliyu
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya ƙaddamar da sabon ofishin ’yan sanda na shiyya da aka gina a Ƙaramar Hukumar Rogo ta jihar.
An gina ofishin ne bisa ƙudurin Shugaban Majalisar, wanda daga bisani ya miƙa shi ga rundunar ’yan sandan Najeriya domin ƙarfafa ayyukan tsaro da inganta aikin ’yan sanda a yankin.
Da yake jawabi yayin bikin ƙaddamar da ofishin, Falgore ya ce gina shi na daga cikin ƙoƙarinsa na tallafa wa hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Rogo da sauran sassan jihar Kano.
Ya bayyana cewa samar da ingantaccen ofishin ’yan sanda zai taimaka wajen inganta ayyukan jami’an tsaro da ƙarfafa yaƙi da laifuffuka da sauran ƙalubalen tsaro.
A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Muhammad Bakori, ya bayyana ofishin a matsayin wani muhimmin ƙari ga ababen more rayuwar tsaro a jihar.
Ya yaba wa Shugaban Majalisar bisa wannan ƙoƙari, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa tsarin aikin ’yan sanda tare da haɗin gwiwar al’umma, kuma ya kamata sauran shugabanni su yi koyi da shi.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa bikin ƙaddamar da ofishin ya samu halartar ’yan majalisa, manyan jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren tsaro.
-
Labarai5 days agoJigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a
-
Labarai3 days agoNIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu
-
Labarai4 days agoGobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara
-
Labarai1 day agoINEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna
-
Labarai5 days agoZa a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna
-
Labarai2 days agoAn Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki
