Connect with us

Labarai

Za a bada tallafin kayan Miliyan 250 ga wadanda rikici ya shafa a Jos

Published

on

Asusun tallafawa wadanda wata masifa ta Shafa ya bada gudummuwar kayaking da kudin su ya kai naira miliyan 250 ga al’unmar kananan hukunomin da jihar Plateau da suka hada da Riyom, Bassa da barikin Ladi.

Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang ya fada wajen kaddamar da bada tallafin cewa, zasuyi dukkanin abin da zasu iya don tabbatar tsaron lafiya da dukiyar al’umma.

Asusun Wanda ke karkashin jagorancin Theophilus Danjuma na masu zaman kansu ne da ke mayarda hankali wajen bada tallafin ilimi, tsaftar muhalli da ruwansha da dai sauransu.

Manufar ita ce dai karfafa al’ummomin kananan hukumomin Bassa Riyom da Barikin Ladi da wannan masifar ta Shafa.

Kayayyakin da aka bada tallafi sun hada da kayayyakin abinci da na karatu.

Gwamnan Jihar Plateau yace wata manufar su ita ce mayarda al’ummomin da aka raba da gidajen su na iyaye da kakanni don su ci gaba da noma, saboda gwamnati ba tada nufin ajiye su a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Gwamnan ya Kuma godewa wadanda suka bada wannan tallafi tare da bayyana cewa ya bada umurnin ga sakataren Gwamnatin jihar da ya kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai bibiyi dukkanin abubuwan da za ayi don tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon kaya.

Jami’ar ayukka ta Asusun Mrs. TOYOSI Akenrele Ogunsiyi ta bayyana cewa suna sane da duk wani kalubale da ake fuskanta, sai dai ba za ta iya Kamala aikin Nan.

Shugabar asusun wacce ta bayyana al’ummar jihar Plateau a matsayin masu hazaka tace zasu talafawa dukkanin masu kasuwanci domin bunkasa harkokin su.

Mrs. Akenrele Ogunsiyi tace zasu mayarda hankali wajen ganin cewa sunyi aiki da duk Wanda ya rike aikinsa da gaskiya tare da hukunta wadanda suka kasa yin aikin da aka sa su

Shi Kuma shugaban hukunar bada agajin gaggawa na jihar Mr. Sunday Abudu ya bada tabbacin cewa za ayi adalci wajen rabon kayan tallafin.

Josiah Buzum/Shafii Wababe

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai26 mins ago

Muna Mika Sakon Ta’aziyar Mu Ga Al’ummar Iran – Tinibu

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa rasuwar shugaba Ebrahim Raisi;...

Fasaha2 hours ago

Gwamnan Kaduna Ya Kaddamar Da Sabbin Ajujuwa A Zaria

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya kaddamar da rukunin ajujuwa 18 a makarantun Basic Education guda biyu dake karamar hukumar...

Fasaha3 hours ago

Shugaban Kasa Ya Kaddamar Sabon Birnin Kasuwanci A Abuja

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da samarda wani da za a samar don gudanarda harkokin kasuwanci a cikinsa da...

Labarai3 hours ago

Kungiyar CAN Ta Rasa Mata Shida A Hadarin Mota A Taraba

An bayyana cewa wasu ’yan kungiyar mata ta kungiyar Kiristoci ta Najeriya (WOWICAN) su shida ne suka rasa rayukansu a...

Labarai3 hours ago

‘Yan Sakai Jihar Taraba Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa

Rundunar ‘yan banga ta Najeriya (VGN) reshen jihar Taraba ta yi nasarar ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa...

Ilimi4 hours ago

Talatar Nan Jirgin farko na Maniyatan jihar Kwara Zai Tashi

An dage tashin jirgin farko daga filin jirgin sama na Janar Tunde Idiagbon na kasa da kasa na Ilorin don...

Labarai4 hours ago

HARIN MASALLACIN KANO: Obi Ya Ziyarci Wadanda Ke Asibiti

  Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya ziyarci wadanda kona masallacin Kano...

Labarai4 hours ago

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi Ta Yi Kiran A Yiwa Mijinta Addu’a

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasir Idris, ta ce addu’a ita ce ginshikin duk wani shugabanci mai nasara, don...

Labarai4 hours ago

Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitin Kwanar Ganduje A Kano

Gwamnatin jihar Kano, ta rufe tare asibitin Kwanar Ganduje dake unguwar Sharada Karamar Hukumar Kano Municipal.   Babban daraktan hukumar...

Labarai5 hours ago

Shugaban Iran Ebrahim Raisi Ya Rasu A Hatsarin Jirgi

Jami’an Iran sun ce Shugaba Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar, Hossein Amir-Abdollahian sun rasu a wani hatsarin jirgin...

Mafi Shahara