Kasuwanci
Masu Sayar da Rago Sun Koka A Zamfara Saboda Karancin Masaya
Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni.
Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau.
Malam Gusau ya bayyana cewa, duk da cewa ana samun raguna da yawa, amma an samu karancin masu saye.
Sai dai ya bayyana fatan cewa lamarin zai iya gyaruwa yayin da bukukuwan Sallah ke kara gabatowa.
“Amma idan abubuwa sun ci gaba da haka, to gaskiya, akwai matsala ta gaske,”
“Har yanzu, na yi imani cewa da sauran kwanaki abubuwa za su iya canzawa, in sha Allah.”
Malam Saidu Gusau ya bayyana cewa, kungiyar ta yi kokarin ganin an samu rago musamman saboda kalubalen da ke tattare da rufe iyakokin kasar ta Jamhuriyar Nijar.
“Lokacin da shugaban kasar Nijar ya bayar da umarnin rufe iyakokin, hakan na nufin ba za a iya fitar da raguna zuwa wasu kasashen Afirka ba, shi ya sa muka yi nisa wajen ganin an shigo da raguna a cikin Zamfara domin jama’a su yi Sallar Idi cikin sauki.”
Shugaban ya koka da karin farashin kananan raguna idan aka kwatanta da shekarun baya.
“A shekarar da ta gabata, an sayar da mafi kankantar ragon da ya dace da hadaya a kan kudi kusan #40,000, amma a bana, ko da mafi kankantar farashinsa ya haura ₦100,000.”
“Yanzu awaki suna farawa daga ₦55,000 zuwa ₦60,000 zuwa sama, yayin da raguna mafi arha ke kan ₦70,000.”
Ya bayyana cewa, a karon farko a tarihin kasuwar dabbobi ta Gusau, an sayar da rago sama da Naira miliyan 1 a bana.
“A da, muna kai irin wadannan raguna masu kima ne kawai zuwa wasu kasuwanni inda masu siya za su iya sayen su, amma a bana, mun sayar da guda daya a kasuwarmu.”
Malam Saidu Ibrahim Gusau ya kuma yi kira ga ’yan uwansu masu sayar da raguna da su rika gudanar da sana’arsu da ikhlasi da tsoron Allah domin samun albarkar Ubangiji.
Wani mazaunin garin Gusau da ya isa kasuwar domin siyan rago da naira 50,000 ya nuna damuwar rashin samun haka.
Ya shaida wa wakilin gidan rediyon Najeriya cewa ya canja ra’ayinsa na sayen zai yi amfani da kudin ya sayi masara ga iyalansa.
Wani mai siyan rago a kasuwar ya ce abin da yake sa ran a duk shekara shi ne, za a iya kara farashin raguna, ya kuma shawarci kowa da ya rika kula da dabbar da zai iya samu.
COV/AMINU DALHATU.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
