Connect with us

Kasuwanci

Ana samun Karancin Masu Sayen Dabbobi A Kano Duk Da Gabatowar Sallar Layya

Published

on

Dillalan rago a jihar Kano sun nuna damuwarsu kan rashin zuwan masaya da suke fuskanta duk da ‘yan kwanaki da suka rage ayi bukukuwan Sallah.

 

Ziyarar da aka kai kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa ta nuna cewa, da yawa daga cikin masu sayar da kayayyaki sun shafe tsawon yini ba tare da yin cinikin komai ba, inda masu saye kadan ke zuwa sayen dabbobin hadaya.

 

Da yake zantawa da gidan rediyon Najeriya shugaban kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa, Alhaji Yusuf Ahmed Muhammad ya bayyana cewa duk da cewa mutane na zuwa kasuwar domin tambayar farashin, amma a zahiri kadan ne ke saye.

 

Ya bayyana cewa yayin da wasu kwastomomi ke siyan kananan raguna da farashinsu ya kai tsakanin ₦80,000 zuwa 150,000, da yawa ba sa iya sayen manyan raguna.

 

A cewar Alhaji Yusuf, farashin raguna ya tashi daga ₦80,000 zuwa miliyan 1, shanu daga ₦250,000 zuwa miliyan 2, rakuma daga ₦500,000 zuwa ₦1 miliyan.

 

Ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar da ake ta yadawa game da tsadar kayayyaki, inda ya kara musu kwarin gwuiwa maimakon su ziyarci kasuwa su gani da kansu.

 

“Kamar yadda kuke gani mutane kadan ne ke tsaye kusa da wasu dabbobi suna neman farashi amma a karshe yawancinsu suna barin ba tare da siya ba”

 

Wani dillalin dabbobi, Alhaji Anas Garba Abubakar, ya bayyana cewa a shekarun baya miliyan 2 na iya sayen raguna sama da ashirin daga kasuwannin cikin gida. “Amma a wannan shekara, za ku iya samun kusan raguna biyar kawai a kan adadin,” in ji shi.

 

Ya alakanta tashin farashin da dalilai kamar hana shigo da rago daga Nijar da kuma tsadar kayan abinci da ake ci gaba da yi, wanda har yanzu ba a samu canji ba duk da faduwar farashin kayan abinci a fadin kasar.

 

Masu son siyan kayayyaki Abdullahi Kabir da Bashir Ibrahim Hassan su ma sun bayyana nasu bayan sun ziyarci kasuwar. “Mun zo nan don siyan raguna, amma kamar yadda kuke gani, dole ne mu koma gida mu sake shiryawa. Farashin ya yi tsada sosai.”

 

Sun bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki da su dauki matakin gaggawa don hana faruwar lamarin.

 

A al’adance dai, kwanaki masu gabatowa da Sallar Idi, kasuwannin dabbobi sun cika da masu saye da sha’awar sayen dabbobin hadaya.

 

KHADIJAH ALIYU

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara