Labarai
‘Yan Sanda Sun Kama Wani Gungun Masu Satar Motoci A Nasarawa
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Nasarawa ta cafke wasu gungun masu satar motoci tare da dawo da wata mota da aka sace.
A cikin wata sanarwa da Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda, SP Ramhan Nansel ya fitar, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a cikin wannan aika-aika, a kan hanyar Doma zuwa Lafia, bisa sahihan bayanan sirri.

Sanarwar ta kara da cewa, ana zargin waɗanda ake tuhuma da haɗa kai wajen satar mota da bindiga a Jihar Enugu, inda suka kwace wata mota kirar Toyota Venza mai launin baki da karfin bindiga.
Sanarwar ta bayyana cewa, saboda saurin tattara bayanan sirri da haɗin gwiwar jihohi ba tare da tangarda ba, an kama waɗanda ake zargin a yankin hanyar Doma zuwa Lafia, kuma an gano motar da aka sace nan take.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Shattima Jauro Mohammed, ya bayyana wannan nasara a matsayin babban ci gaba a yaƙi da satar motoci da aka tsara, inda ya jaddada kudirin rundunar wajen ganin cewa an dakile miyagun laifuka cikin gaggawa kuma an gurfanar da masu laifi.
Ya yabawa ƙwazon jami’an da suka gudanar da wannan aiki tare da tabbatarwa al’umma cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Waɗanda ake zargin suna tsare a halin yanzu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike don gano sauran abokan aikinsu da kuma gano sauran abubuwan da aka sace.
Daga Aliyu Muraki
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
