Labarai
NUPENG Ta Dakatar Da Yajin Aiki Bayan Kulla Yarjejeniya Da Dangote
Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Kasa (NUPENG), ta dakatar da yajin aikinta bayan kulla yarjejeniya da mahukunta matatar man fetur ta Dangote kan haƙƙin ma’aikata na shiga ƙungiyar kwadago.
NUPENG ta fara yajin aikin ne don nuna adawa da kin amincewar matatar Dangote kan shigar ma’aikatanta ƙungiyoyi.
An cimma matsayar ne bayan taron sulhu da aka gudanar a Abuja, wanda Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Mohammad Dingyadi, ya jagoranta, inda ɓangarorin biyu suka rattaba hannu kan Takardar Yarjejeniya.
Takardar yarjejeniyar ta samu sa hannun Darakta a matatar ta Dangote Sayyu Dantata, Shugaban NUPENG, Kwamared Akporeha Williams, da wasu shugabannin ƙungiyar.
A cikin yarjejeniyar, NUPENG ta amince da dakatar da yajin aikin nan take, domin buɗe hanya ga ci gaba da tattaunawa kan haƙƙoƙi da walwalar ma’aikata a matatar man fetur din ta Dangote.
RN
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
