Labarai
Za A Yi Jana’izar Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ranar Talata A Garin Daura
Za a yi jana’izar tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari a garinsa na Daura da misalin ƙarfe biyu na rana gobe a Talata.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda ne ya sanar da hakan a Katsina yayin da yake yi wa manema labarai bayani game da shirye-shiryen jana’izar tsohon shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa an kammala shirye-shiryen ne bayan tattaunawa da iyalan marigayin da kuma abokansa na kusa.
Gwamnan ya ƙara da cewa za a iso da gawar tsohon shugaban ƙasa ne a gobe Talata daga birnin London zuwa Daura.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Muhammadu Buhari, al’ummar Jihar Katsina da kuma sauran ‘yan Najeriya bisa rasuwar wannan dattijo, inda ya yi kira ga jama’a da su yi masa addu’a.
“Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya sada shi da rahamaSa, Ya sa Aljannatul Firdaus makomarsa.
“Haka kuma muna miƙa ta’aziyyarmu ga shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunonin tsaron ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa rasuwar wanda ya gada. Allah Ya ba mu ƙarfin ɗaukar wannan babban rashi,” in ji Gwamna.
Daga Isma’il Adamu
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
