Connect with us

Labarai

An Yi Kiran Karfafa Hadin Gwiwa Don Magance Cutar Haukan Kare A Zamfara

Published

on

Daga Aminu Dalhatu, Gusau

Hukumar Bunƙasa Kiwo ta Jihar Zamfara ta yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin yaƙi da cutar hauka tare da hana mace-macen da cutar ke haddasawa.

Babban Daraktan Hukumar, Dakta Isma’ila Usman Gusau, ya yi kiran ne a lokacin bikin Ranar Cutar hauka ta Duniya ta shekarar 2026 a Gusau, wanda ya ƙunshi jerin gwanon wayar da kai da kuma ƙaddamar da shirin rigakafin cutar kyauta a Fadar Mai Martaba Sarkin Gusau.

Ƙungiyar Likitocin Dabbobi ta Najeriya, NVMA, reshen Jihar Zamfara ce ta shirya gangamin wayar da kan jama’a, wanda ya haɗa ƙwararrun likitocin dabbobi, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙara wayar da kan jama’a da kuma inganta haɗin gwiwar yaƙi da cutar.

Da yake jawabi a wajen taron, Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa Kiwo ta Jihar Zamfara, Dakta Isma’ila Usman Gusau, ya ce an shirya gangamin ne domin neman goyon bayan Masarautar Gusau da sauran hukumomin gargajiya wajen yaƙi da cutar.

Dakta Gusau ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma da kuma ƙarfafa masu kiwon dabbobi su riƙa kula da dabbobinsu yadda ya kamata tare da tabbatar da yi musu rigakafi akai-akai.

Shi ma da yake jawabi, Mai Kula da Shirin L-PRESS na Jihar Zamfara, Nasiru Mohammed, ya yi alƙawarin cewa shirin zai ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen bunƙasa kiwo da kula da lafiyar dabbobi a jihar.

Nasiru Mohammed ya ce lafiyar dabbobi na daga cikin muhimman abubuwan da shirin L-PRESS ya mayar da hankali a kai, musamman a ƙarƙashin ɓangare na ɗaya, ƙaramin ɓangare na 1.3, wanda ya mayar da hankali kan ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar dabbobi.

A nasa jawabin, Daraktan Ayyukan Kula da Lafiyar Dabbobi na Jihar Zamfara, Dakta Aminu Abdulrazak, ya bayyana cutar hauka a matsayin wata mummunar cuta da ke iya yaɗuwa daga dabbobi zuwa mutane, yana mai jaddada cewa rigakafi na da matuƙar muhimmanci wajen kare mutane daga cutar.

Dakta Abdulrazak ya bayyana cewa karnukan da suka kamu da cutar hauka na iya sauya halayensu, kamar rashin natsuwa da tashin hankali da yawan fitar yawu da cizon mutane ba tare da dalili ba da kuma tsoron ruwa.

Daraktan ya shawarci jama’a da su guji kusantar dabbobin da ake zargin sun kamu da cutar, tare da gaggauta neman kulawar likita idan dabba ta cije su ko kuma suka yi mu’amala da dabbar da ake zargin tana ɗauke da cutar.

Tun da farko, Mai Martaba Sarkin Gusau, Dakta Abdulkadir Ibrahim Bello, ya tabbatar da cewa zai tattauna da sauran sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki kan buƙatar haɗa ƙarfi wajen ilmantar da jama’a da wayar da kansu game da illolin cutar hauka.

Dakta Bello ya ce tun da cutar hauka cuta ce mai kisa wadda za ta iya haddasa asarar rayuka, ya zama wajibi sarakunan gargajiya su yi aiki kafada da kafada da hukumomin da abin ya shafa domin taimakawa wajen dakile cutar da kuma kawo ƙarshenta.

Jerin gwanon wayar da kan jama’ar ya fara ne daga Hukumar Bunƙasa Kiwo ta Jihar Zamfara, inda ya ƙare a Fadar Mai Martaba Sarkin Gusau, Dakta Abdulkadir Ibrahim Bello, inda aka ƙaddamar da shirin rigakafin cutar haukan kare kyauta a hukumance.

Fasara; Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara