Connect with us

Labarai

Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda A Kaduna

Published

on

Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Mahara Bakwai Tare Da Kame Makamai Da Babura A Jihar Kaduna.

 

Dakarun runduna ta daya ta sojojin Najeriya da aka girke a wani shingen a Udawa sun gudanar da sintiri na yaki a hanyar Udawa zuwa Kurebe a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a ranar 19 ga watan Mayu.

 

A wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya ta Kaduna, Laftanal Kanal Musa Yahaya ya fitar, ya ce a lokacin da suke sintiri da sojoji sun yi gaba da gaba da ‘yan ta’addan inda suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyar.

 

Hakazalika, dakarun rundunar da aka tura a Sabon Birni a karamar hukumar Igabi, sun tare wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin Baka, inda suka yi ta harbe harbe da bindiga mai karfin gaske, inda suka gudu zuwa tsaunin da ke kusa da su dauke da raunukan harbin bindiga da dama.

 

Haka kuma, a lokacin da suke kwanto a kauyen Kwaga da ke karamar hukumar Birnin Gwari, sojojin sun kashe ‘yan ta’addan biyu daga cikinsu.

 

Wasu kayayyakin da aka kwato a ayyukan sun hada da bindiga guda daya, harsashi shida,  bindiga kirar AK 47 daya, babura biyu, da dai sauransu.

 

A cewar sanarwar, babban kwamandan runduna ta daya kuma kwamandan Operation WHIRL PUNCH, Manjo Janar Landers Saraso, ya yabawa sojojin bisa yadda suka yi tsayin daka kuma ya umurce su da su ci gaba da wannan namijin kokari don kakkabe ‘yan ta’adda daga kasan nan.

 

Hakazalika ya kuma yi kira ga duk ‘yan kasa masu bin doka da oda da su kai rahoton mutanen da aka gani da raunukan harbin bindiga suna neman kulawa ga rundunar sojojin Najeriya ko kuma hukumomin tsaro mafi kusa.

 

Sanarwar ta yi kira ga al’ummar jihohin Kaduna da Neja da su baiwa rundunar soji da sauran jami’an tsaro damar samun bayanan sirri a kan lokaci da kuma matakan da suka dace domin daukar matakin gaggawa.

 

PR/Usman Sani/Wababe

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara