Labarai
Niger Ta Yi Umurnin Kama Duk Wanda Yake Yunkurin Tada Zaune Tsaye
Gwamnatin Jihar Neja ta yi gargadin cewa daga yanzu duk wani matashi ko gungun jama’a da aka samu da hannu wajen tashe-tashen hankula da hana zaman lafiya a Minna babban birnin jihar da kewaye za a kama su.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida Birgediya Janar, Garba Abdullahi Mohammed wanda ya yi wannan gargadin a wata tattaunawa ta wayar tarho da Rediyon Najeriya a Minna ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da hukunta duk wasu masu tada zaune tsaye.
Birgediya Janar Garba Abdullahi Mohammed ya ci gaba da bayanin cewa za a hukutan duk wani mutum ko maai girman sa da aka samu da yunkurin belin duk wani bata gari da aka kama.
Ya ce gwamnatin jihar ba za ta nade hannunta ba sannan ta bar miyagu su lalata rayuka da dukiyoyin ‘yan Nigeriya da ke gudanar da sana’o’insu na halal.
Kwamishinan yana mayar da martani ne game da tashe-tashen hankula da matasan suka yi a Minna musamman wanda ya faru kwanan nan inda aka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu a wani turmutsitsi tsakanin kungiyoyin matasa biyu a Maotumbi da ke karamar hukumar Bosso a jihar Neja. .
Kwanaki uku da suka gabata wasu matasa da suka addabi yankin Fadikpe ne suka kashe wani ma’aikacin lafiya mai suna Umar a lokacin da suke dawowa daga aiki, inda suka ce hakan bai dace ba kuma ya shawarce su da su daina ko kuma su fuskanci fushin doka.
A halin da ake ciki dai an tsaurara matakan tsaro a yankunan da ake fama da tashin hankali da kuma wasu sassa na Minna babban birnin jihar domin ganin an fara samun tashe-tashen hankulan matasa, tada zaune tsaye da kuma nuna kyama.
KARSHEN ALIYU LAWAL/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
