Ilimi
Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Kidayar Jama’a Na Kasa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da wani babban kwamiti kan kidayar jama’a da gidaje mai zuwa, inda ya umurci mambobin su gabatar da rahoton farko cikin makonni uku.
Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, a wajen taron da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce kidayar na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da kuma tsare-tsare na gaskiya.
Ya lura cewa ingantaccen bayanan yawan jama’a yana da mahimmanci don yanke shawara mai inganci a cikin manyan sassan kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro, da kuma tsara tattalin arziki.
Shugaban ya jaddada cewa, an gudanar da kidayar jama’a ta karshe a shekarar 2006, wato kusan shekaru ashirin da suka wuce, kuma tun daga lokacin ne Najeriya ta fuskanci sauye-sauye a yawan al’umma, matsugunan jama’a, da kuma muhimman abubuwan da suka shafi kasa baki daya.
Ya kuma jaddada mahimmancin tsarin da aka yi amfani da shi na fasaha don tabbatar da sahihin sakamako mai inganci, inda ya bayyana bukatar yin hadin gwiwa a tsakanin dukkanin hukumomin da abin ya shafa, da suka hada da hukumar kidaya ta kasa, da hukumar kula da shaida ta kasa NIMC, da ma’aikatar kudi, da ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan kidayar jama’a da gidaje kuma ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Sanata Atiku Bagudu, ya tabbatar da cewa kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin wa’adin makonni uku da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar.
Bello Wakili/Abuja
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
