Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Jinjinawa ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje Bisa Nuna Halin Dattaku

Published

on

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game  kyawawan dabi’u da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi’un da ke kara martabar kasa.

Shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku daga jakadan kasar  Kanada a Najeriya, Pasquale Salvaggio, da jakadan Saliyo, Dr Julius F. Sandy, a fadar gwamnati.

Har ila yau, shugaba Tinubu ya karbi wasikun amincewa da nuna gamsuwa daga Legesse Geremew Haile, jakadan kasar Habasha a Najeriya, da Archbishop Michael Francis Crotty, shugaban Bishop Bishop na fadar Vatican a Najeriya.

Babban Kwamishinan na Kanada ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa ’yan Najeriya suna da himma a fannin ilimi, da wasannin motsa jiki, da kimiyya, da lafiya, da kasuwanci a kasarsa.

Ya ce ‘yan Najeriya a Kanada suna nuna kyawawan dabi’u da wayewa, da kwazo yayin  cimma burinsu.

Salvaggio, wanda a baya ya yi aiki a Ghana da Cote’Ivoire, ya ce Kanada na neman fadada sha’awarta a kan man fetur da iskar gas, da al’amuran da suka shafi fasahar zamani, da noma, a dangantakar ta Najeriya.

Shugaba Tinubu ya yaba da nasarorin da ‘yan Najeriya suka samu a kasashen waje, yana mai bayyana su a matsayin abin zaburarwa ga mutane da dama.

A wani taron da ya yi da babban jakadan Saliyo kuwa, shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa, muradin Najeriya na ci gaban gabar tekun Yamma da Afirka shi ne abin da ya sa a gaba.

Shugaban ya shaida wa jakadan cewa jarin da Najeriya ta yi a Saliyo na tsawon shekaru da dama ya taimaka wajen ci gaban Afirka da kuma inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Jakadan ya godewa shugaban kasar bisa goyon bayan da Najeriya ke bayarwa wajen cigaban kasarsa.

Ya ce “A Saliyo, ‘yan Najeriya sun fi ‘yan kasar  yin kasuwanci, yawancin malamai a makarantu ‘yan Najeriya ne, babu bambanci tsakanin dan Najeriya da dan Saliyo idan kana tafiya a kan titin Freetown.”

Muna bukatar ci gaba da neman zaman lafiya a nahiyarmu, ya kamata mu hada karfi da karfe wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kalubalen da muke fuskanta a Afirka shi ne rashin tsaro, wanda ke hana ci gaba, ba mu da wanda zai kawo mana zaman lafiya, ssai in mun yi aiki tukuru.” in ji shi.

 

Daga Bello Wakili

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara