Labarai
Gwamnatin Kwara Ta Horar Da Manoma Sama Da 500 Tare Da Basu Tallafi
Manoma sama da 500 daga gundumomi 15 na karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu horo kan kiwon awaki na zamani da kuma yadda ake samar da abincin dabbobi, a wani yunƙuri na rage yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya tare da inganta rayuwar al’ummar karkara.
An gudanar da wannan horo a Idofian karkashin haɗin gwiwar karamar hukumar Ifelodun da shirin Livestock Productivity and Resilience Support Project (L-PRES).

Da yake jawabi a wurin taron, mataimakin gwamnan jihar Kwara, Mista Kayode Alabi wanda Honarabul Ganiyu Afolabi, dan majalisar jihar mai wakiltar mazaɓar Omupo ya wakilta, ya jaddada muhimmancin wannan shiri wajen magance matsalolin da manoman karkara ke fuskanta. Ya bayyana cewa shirin ba wai kawai zai rage rikici ba ne, zai kuma ƙara yawan kudaden shiga ga manoma da kuma ƙarfafa cin gashin kansu.

Ya ja hankalin mahalarta da su yi amfani da damar wajen amfani da sabbin ilimin da suka samu domin faɗaɗa sana’arsu da kuma samar da abincin dabbobi cikin sauƙi ta hanyar amfani da shara daga amfanin gona.
Shi ma da yake jawabi, shugaban karamar hukumar Ifelodun, Honarabul Abdulrasheed Yusuf, ya bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma rage kuɗin da ake kashewa wajen kiwon dabbobi ta hanyar samar da abincin dabbobi a cikin gida.

Ya kuma ƙara da cewa karamar hukumar tana aiki tare da masu ruwa da tsaki don samar da muhimman abubuwa kamar ruwa da wasu muhimman abubuwan raya ƙauyuka.
A nasa jawabin, sarkin Igbaja, Oba Ahmed Babalola (Elesie na Igbaja), ya yabawa wadanda suka shirya wannan horo, yana mai cewa an yi shi a lokacin da ya dace. Ya tabbatar wa mahalarta cikakken goyon baya domin nasara da dorewar shirin.

A baya, shugaban shirin L-PRES a jihar Kwara, Mista Olusoji Oyawoye, ya ƙarfafa matasa da su rungumi dama a fannin noma domin su dogara da kansu maimakon jiran aikin gwamnati. Ya buƙaci mahalarta horon da su rungumi shirin da cikakkiyar niyya domin su samu ƙwarewa da za ta taimaka musu da al’ummarsu gaba ɗaya.

Wannan horo wani ɓangare ne na babban shirin L-PRES da ke ƙoƙarin ƙara yawan amfanin kiwo, rage rikice-rikice, da kuma inganta ɗorewar rayuwa a ƙauyuka a faɗin Najeriya.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
