Labarai
Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Dauki Nauyin Aurar Da Mata 300 Kafin Azumi
Gwamnatin jihar Kebbi, ta kammala shirye-shiryen gudanar da daurin auren mata dari uku a karshen watan Fabrairun wannan shekara.

Da yake zantawa da manema labarai da yammacin Lahadi, shugaban babban kwamitin kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Suleiman Muhammad Argungu, ya bayyana cewa, nasarar daurin auren da aka yi a shekarar da ta gabata, wanda gidauniyar NANAS ta uwargidan Gwamnan, Hajiya Nafisa ta shirya, ya sanya gwamnatin ta sami kwarin gwiwar daukar nauyin aurar da wasu rukunin a wannan shekarar.

A cewar Shugaban kwamitin, za a aurar da mutane 600 marasa galihu ba tare da la’akari da addini, kabilanci da siyasa ba a tsarin gwamnati.
Ya ce, an kafa kwamitocin tantancewa a dukkan kananan hukumomi 21 domin zabar ma’auratan da suka cancanta bisa ka’idojin da aka gindaya wadanda suka hada da tabbacin ango yana da abin yi do daukar nauyin iyalansa, da kuma matsugunin da za su zauna.


Suleman Argungu, ya bayyana cewa, dukkan ma’auratan za a yi musu gwajin lafiya na tilas, ciki har da gwajin kwayar cutamai karya garkuwar jiki ta HIV, da kwayoyin halitta na Genotype.
Za a biya Naira 180,000 a matsayin sadaki ga kowace amarya, wanda ya kama jimillar Naira miliyan 54, tare da kayan daki, da suka katifa, gado da kuma kayan amfanin gida.
Daga Abdullahi Tukur
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
