Connect with us

Labarai

CORET, ECOWAS Sun Hada Matasa Da Wasu Abokan Hulda Don Inganta Kiwo Da Madara

Published

on

 

Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwo na Gargajiya ta Afirka (CORET) tare da haɗin gwiwar ECOWAS sun hada matasan da aka horar da su da manyan abokan holda don bunkasa kiyo da bunkasa yawan madara a jihohin Kaduna da Jigawa.

 

A yayin zaman karawa juna sani a Kaduna, Koodinetan Aikin na CORET Dr. Umar Ardo Abdul, ya ce an shirya wannan zama ne domin haɗa matasan da aka horar da su da masu ruwa da tsaki a harkan kiyo da bunkasa yawan madara na gwamnati da masu zaman kansu, domin a horas da su hanyoyin samun aikin yi da kuma bunkasa yawan madara.

 

Wannan shiri na daga cikin Aikin ECOWAS na karfafa samar da ayyukan yi ga matasa da kuma bunkasa darajar madara, wanda yake ɗaukar tsawon shekaru uku, kuma an kaddamar da shi ne domin koya wa matasa ƙwarewar aiki tare da samar musu damar samun kuɗin shiga a cikin fannin kiwo.

 

Koodinetan Aikin, Dr. Umar Ardo Abdul, ya bayyana cewa an yi wa matasa 1,350 rajista a Kaduna da Jigawa.

 

A cewarsa, matasa 26 daga jihohin Kaduna da Jigawa yanzu an haɗa su da masana waɗanda za su tallafa musu a ayyukan yin allurar rigakafi da taimakon lafiyar dabbobi da aikin yaɗa ilimi, da kuma samar da kayan kiwo.

 

Ya yi bayani cewa zaman ya haɗa kwararrun likitocin dabbobi, ma’aikatan yaɗa ilimin kiwo, masu yin dasa ramin maniyyi da masu sarrafa abincin dabbobi da sauran masu ruwa da tsaki a kiwo domin gina ƙaƙƙarfan cibiyar ayyuka.

 

Dr. Umar Ardo ya ce manufar ita ce a tabbatar matasan sun yi amfani da ƙwarewar da suka samu wajen ba da muhimman ayyukan kiwo, samun kuɗin shiga, da kuma tallafawa makiyaya da manoma a yankunansu.

 

Yace ma’aikatar aikin gona ta Jihar Kaduna da Cibiyar Binciken Samar da Dabbobi ta Ƙasa (NAPRI) a matsayin muhimman abokan aikin gwamnati, yana mai cewa NAPRI cibiyar bincike ce da a ke dogaro da ita wajen binciken kiwo, samar da rigakafin dabbobi da kuma kayayyakin kiwo.

 

Koodinetan ya ce gwamnati na da muhimmiyar rawa ta tsare-tsare a fannin kiwon lafiya na dabbobi, rigakafi da kuma samar da kaji, yayin da kamfanonin masu zaman kansu ke taka rawa wajen samar da magungunan dabbobi da kayan kiwo, waɗanda suka zama ginshiƙai ga masu cin gajiyar shirin.

 

Dr. Umar Ardo ya jaddada cewa CORET, a matsayinta na ƙungiyar haɗin kan masu kiwo ta nahiyar Afirka, ta kuduri aniyar cike gibin da ke tsakanin hukumomin gwamnati, cibiyoyin bincike, kamfanoni masu zaman kansu da matasan da aka horar domin inganta harkar kiwo da bunkasa madara.

 

A nasa jawabin, wakilin Hukumar Ilimin Makiyaya ta Ƙasa, Abubakar Lawal Boro, ya ce tsarin PPP (Haɗin Gwiwar Gwamnati da Masu Zaman Kansu) shi ne ginshiƙin cigaban kiwo mai ɗorewa, domin gwamnati na samar da tsarin aiki da jagoranci, yayin da kamfanoni ke samar da muhimman kayayyaki.

Ya yi kira ga iyalan makiyaya su bai wa ilimi muhimmanci ta hanyar mayar da ‘ya’yansu makaranta, yana nuna damuwa kan yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta da tasirin rashin tsaro ga yunkurin wayar da kai.

 

Ɗaya daga cikin mahalarta, Anas Ibrahim, ya bayyana wannan horo a matsayin mai matuƙar amfani kuma ya zo a kan lokaci.

 

Ya ce zaman ya kasance cikin tsari kuma yana ɗaya daga cikin mafi inganci da suka halarta, inda ya faɗaɗa musu fahimtar lafiyar dabbobi, kula da abincin kiwo, da hulɗa da masu samar da ayyukan kiwo.

 

Wani mahalarta kuma, Rabiu Adamu daga Ladugga, ya yaba wa CORET da abokan aikinta bisa samar da dandalin da ya bai wa masu kiwo damar samun damar magungunan dabbobi masu inganci, abincin kiwo, da iri na kiwo da za su inganta kiwon madara.

COV: Adamu Yusuf

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara