Labarai
An Bukaci Sarakuna Su Ci Gaba Da Yiwa Al’umma Aiki
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Danladi Jatau, ya bukaci sarakunan gargajiya da su ci gaba da karfafa hadin kai da zaman lafiya a yankunansu domin samun ci gaba a jihar.
Shugaban majalisar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin murnar cika shekaru 5 akan mulki da kuma murnar cika shekaru 50 da haihuwar HRH, Chim Nku, Mista Habila Adamu Aboki a karamar hukumar Akwanga.
Mista Danladi Jatau, wanda ya bayyana muhimmancin hadin kai da zaman lafiya ga ci gaban al’umma, ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da su ci gaba da sasanta al’ummarsu domin zaman lafiya.
Ya taya sarkin mai daraja ta biyu murnar tare da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya da kariya da kuma hikima a shekaru masu zuwa.
Shugaban majalisar ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da addu’a tare da marawa Gwamna Abdullahi Sule da sauran shugabannin baya domin samun nasara.
Tun da farko, HRH Mista Habila Adamu Aboki, Chim Nku, ya ce ya yanke shawarar shirya taron ne domin ya gode wa Allah a kan rayuwarsa da ta ’yan uwa.
Ya kuma yabawa Gwamna Abdullahi Sule da sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki da sauran jama’a bisa goyon bayan da suke ba shi don samun nasara.
Basaraken ya yi amfani da wannan damar wajen tabbatar da aniyarsa na inganta hadin kai da zaman lafiya a tsakanin talakawansa.
COV/Aliyu Muraki/Lafia./Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
