Labarai
Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Jigawa
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kaddamar da hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa a jihar.
Yayin jawabinsa a wajen bikin kaddamar da hukumar, Gwamna Umar Namadi ya jaddada mahimmancin hukumar wajen yaki da cin hanci da rashawa domin tsaftace ayyuku a jihar.
Ya kuma bukaci mambobin hukumar da su yi aiki bisa doka ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.
“Kada ku bari bukatun ku su yi tasiri a ayyukanku, haka kuma babu wanda zai tsoma baki cikin ayyukanku daga bangaren gwamnati.” Inji Gwamnan
Malam Umar Namadi ya kuma bukaci hukumar da ta kiyaye ka’idojin aiki, tare da yin adalci dm wajen magance korafe-korafen da aka kawo mata.
A jawabinsa, shugaban hukumar Barista Salisu Abdu, ya nuna jin dadinsa ga Gwamna Namadi bisa bashi damar jagorantar hukumar.
Ya kuma tabbatar wa da al’umma kudurin hukumar na tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyukanta.
“Hukumar za ta tabbatar da manufar Gwamna Namadi na samar da sabuwar Jihar Jigawa ba tare da cin hanci da rashawa ba, mun yi alkawarin yin aiki bisa gaskiya da amana ba tare da son zuciya ba.”
Gidan Rediyon Najeriya Kaduna ya ruwaito cewa, an dorawa hukumar korafe-korafen al’umma da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar alhakin binciken ma’aikatu da hukumomin gwamnati na jiha da kananan hukumomi da ma ma’aikatan jihar baki daya.
An rantsar da sabon shugaban hukumar Barista Salisu Abdu tare da sauran mambobin hukumar na dindindin da suka hada da Musa Kallamu Uba Auyo da Hassan Hashim, a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Dutse.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
