Connect with us

Labarai

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Published

on

Daga Aliyu Lawal

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana, biyo bayan tabbatar da bullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Murtala Muhammad Bagana ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Minna, inda ya ce matakan da jihar ta ɗauka na rigakafi ne, domin ƙarfafa sa-ido, gano masu ɗauke da cutar da wuri, da kuma ɗaukar matakan gaggawa idan an samu wanda ake zargi da kamuwa da ita.

Dakta Bagana ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa har yanzu ba a gano ko da mutum ɗaya da ya kamu da cutar Ebola a Jihar Nijar ba.

Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta fitar a ranar Talata, 20 ga Oktoban 2026, inda ta tabbatar da samun wacce  ta kamu da cutar Ebola, wadda ta shigo Najeriya daga Uganda. A halin yanzu, an keɓe ta, inda take samun kulawar jinya, yayin da hukumomin lafiya ke sa-ido kan mutane 44 da aka gano sun yi mu’amala ta kusa da shi.

Kwamishinan ya ce yawan zirga-zirgar mutane da harkokin kasuwanci tsakanin Jihar Nijar da Babban Birnin Tarayya Abuja ya sa ya zama wajibi jihar ta ƙara tsaurara matakan sa-ido da shirin ko-ta-kwana.

Ya ƙara da cewa ma’aikatar na aiki tare da Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC), Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa domin tabbatar da shirye-shiryen tunkarar cutar a faɗin jihar.

Dakta Bagana ya ce an umurci dukkan cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu a Jihar Nijar da su gaggauta kai rahoton duk wanda ake zargin ya kamu da cutar Ebola domin a gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace.

Ma’aikatar ta fitar da lambobin wayar gaggawa da za a kira domin kai rahoton waɗanda ake zargin sun kamu da cutar kamar haka: Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a, 0703 458 3079; Masanin Cutar Annoba na Jiha, 0807 721 3070; Jami’in Sa-Ido da Sanar da Cututtuka na Jiha (DSNO), 0807 529 1989; da kuma layin kyauta na NCDC na ƙasa, 6232.

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara