Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
Daga Bello Wakili
Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a, bayan tabbatar da bullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana cewa matar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar ta shigo Najeriya kwanan nan ta jirgin sama daga Uganda, kuma a halin yanzu an keɓe ta don samun kulawar likitoci.
Ya ce an fara aikin gano mutanen da suka yi mu’amala da matar, inda aka gano mutum 44 da za a sanya ido a kansu domin hana yaɗuwar cutar. Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, da Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) da hukumomin lafiya na Birnin Tarayya suna aiki tare domin shawo kan cutar.
Ministan ya buƙaci cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu, da su ƙarfafa sa ido kan cututtuka, su keɓe waɗanda ake zargin sun kamu da Ebola cikin gaggawa, tare da bin ƙa’idojin kariya daga yaɗuwar cututtuka.
Ya bayyana cewa Ebola tana yaɗuwa ne ta hanyar taɓa jini ko zufar jikin mutumin da ya kamu da cutar kuma alamunta suka bayyana, ko kuma ta hanyar taɓa kayayyakin da suka gurɓata.
Ya shawarci ’yan Najeriya da su riƙa wanke hannuwansu yadda ya kamata, su guji hulɗa da waɗanda ake zargin sun kamu da cutar, tare da kai rahoto ga hukumomin lafiya idan akwai zargin kamuwa da cutar.
Farfesa Pate ya buƙaci mutanen da jami’an lafiya suka tuntuɓa yayin aikin gano waɗanda suka yi mu’amala da mai cutar su ba da haɗin kai. Ya kuma shawarci duk wanda ya fara nuna alamun cutar da ya nemi shawarar jami’an lafiya kafin zuwa asibiti.
Ministan ya tabbatar da cewa Najeriya tana da ƙwarewar tunkarar cutar, bayan nasarar shawo kan barkewar Ebola a shekarar 2014.
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu, su riƙa yaɗa sahihan bayanai, tare da ba da haɗin kai.
Za a iya kiran cibiyar NCDC kyauta ta lamba 6232 domin samun bayanai ko kai rahoton wanda ake zargin ya kamu da cutar.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
