Fasaha
NASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
Daga Yusuf Zubairu
Hukumar Bunƙasa Kayayyakin Kimiyya da Aikin Injiniya ta Ƙasa (NASENI) ta ƙarfafa horar da sana’o’i, fasahar jiragen sama marasa matuƙi da tallafa wa al’umma a Jihar Kaduna, domin bunƙasa ƙwarewar cikin gida da samar da damarmakin tattalin arziki.
Shirye-shiryen sun haɗa da aza harsashin ginin Cibiyar Bunƙasa Ƙwarewar Sana’o’i a Rigachikun, ƙaddamar da cibiyar horar da masu sarrafa jiragen sama marasa matuƙi, da rabon kayayyakin tallafi ga al’umma.
Mataimakin Shugaban NASENI, Khalil Suleiman Halilu, ya ce cibiyar horar da sana’o’in da ake ginawa a Ƙaramar Hukumar Igabi za ta samar da horon aikace-aikace domin bunƙasa ayyukan yi, kasuwanci da dogaro da kai tsakanin matasa.
A wajen ƙaddamar da Cibiyar Horar da Masu Sarrafa Jiragen Sama Marasa Matuki ta NASCAV a Cibiyar Fasahar Sojojin Sama ta Najeriya (AFIT), Kaduna, Halilu ya ce cibiyar ta riga ta horar da rukuni biyu ta hanyar haɗin gwiwar NASENI da Caverton Helicopters.

Gwamna Uba Sani ya miƙa Takardar Shaidar Mallakar Ƙasa (Certificate of Occupancy) ga Babban Mataimakin Shugaban Hukumar NASENI Khalil Suleiman Halilu, yayin bikin aza harsashin ginin Cibiyar Bunƙasa Ƙwarewar Sana’o’i ta hukumar a Rigachikun, Ƙaramar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa fasahar jiragen sama marasa matuƙi za ta taimaka a fannonin noma, sa ido kan ababen more rayuwa, kiwon lafiya, kula da muhalli da tsaro.
Khalil Suleiman ya ce an tsara shirye-shiryen ne domin inganta rayuwar iyalai, rage kashe kuɗaɗen, da bunƙasa ƙwarewar cikin gida.

A bayaninsa, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce cibiyar za ta ƙara inganta koyar da sana’o’in hannu, musamman ga mata, masu buƙata ta musamman da al’ummomin da ba sa samun isasshiyar kulawa. Ya bayyana cewa ɗalibai 4,050 ne suka kammala horo a cibiyar koyar da sana’o’in jihar a watan Agusta, inda gwamnati ta ware naira miliyan 800 domin tallafa musu wajen kafa sana’o’insu.
Gwamna Uba Sani ya ce mata na da muhimmiyar rawa a shirin horar da masu sarrafa jiragen saman, inda ya bayyana cewa aƙalla kashi 60 cikin 100 na mahalarta horon mata ne.
Shi ma Kwamandan AFIT, Air Vice Marshal Adeniran Kolade Ademuwagun, ya yi kira da a ƙara zuba jari wajen bunƙasa fasahar cikin gida domin rage dogaro da kayayyakin ƙasashen waje.
NASENI ta raba murhunan girki masu amfani da makamashi mai tsafta, na’urorin hasken rana na samar da wutar lantarki ga gidaje da sauran kayayyakin tallafi ga mata 450 da maza 50 a jihar.
Jami’an sun kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da kuma amfani da cibiyoyin da kayayyakin tallafin yadda ya kamata domin tabbatar da dorewar amfaninsu ga matasa da al’umma.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
