Connect with us

Labarai

NSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara

Published

on

Daga Aminu Zamfara

Hukumar Tsaro ta NSCDC ta Jihar Zamfara ta kama wani mutum mai shekaru 25, mai suna Bala Abubakar, bisa zargin safarar mutane da tilasta wa yara ƙwadago a Gusau, babban birnin jihar.

Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na hukumar, ASCI Umar Mohammad ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a Gusau, a madadin Kwamandan hukumar na jihar, Sani Mustapha.

Ya ce jami’an NSCDC sun tare wanda ake zargin a yankin Lalan da ke Gusau da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare, ranar 15 ga watan Oktoban 2026, inda suka ceto wasu ’yan mata biyu masu shekaru 13.

’Yan matan da aka ceto, Amira Baje Ibrahim da Haulatu Shaibu, dukkaninsu ’yan asalin ƙaramar hukumar Zurmi ne da ke Jihar Zamfara.

 A cewar Umar Mohammad, binciken farko ya nuna cewa ana zargin ana safarar ’yan matan ne daga ƙaramar hukumar Shinkafi, domin miƙa su ga wasu mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Hadiza da Bara’atu a Suleja, Jihar Neja.

Bayan wannan samame, Kwamandan NSCDC na jihar, Sani Mustapha, ya bayar da umarnin miƙa lamarin ga Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) domin gudanar da ƙarin bincike da ɗaukar matakan shari’a da suka dace.

Kakakin hukumar ya sake jaddada matsayar NSCDC ta rashin amincewa da aikata laifuka, tilasta wa yara ƙwadago da take haƙƙin ɗan Adam, yana mai cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu idan bincike ya tabbatar da hujjojin da suka dace.

Ya kuma buƙaci al’umma da su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa, tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga hukumomin tsaro, domin taimakawa wajen yaƙi da safarar mutane da kuma kare yara masu rauni.

Fassara: Safiyah Abdulkadir 

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara